Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Muggan ƙwayoyi ta ƙasa reshin jihar Nasarawa ta ce a cikin watan Mayun shekarar 2025 da ake ciki kaɗai ta kama sama da masu laifin shan muggan ƙwayoyi da fataucin su inda ta ƙwato sama da muggan kwayoyin kilo 4,764.893 duka a cikin watan Mayun shekarar nan.
Kwamandan hukumar a jihar ta Nasarawa Dechi Elisha Daɓid ne ya bayyana haka a lokacin da yake zanta da manema labarai a sakatariyar hukumar dake Lafiya Babbar birnin jihar ranar Alhamis na makon da ya gabata.
Ya ce, waɗanda jami’an nasa suka cafke da laifin sun hada da wani maisuna Welman Kengbo mai shekaru 60 wanda aka kama a yankin Karu da buhunan tabar wiwi da yawan su yakai kilo 594.8 da Godwin Obi shekaru 39 shima a Karu da aka kama da buhu 4 da rabi na tabar wiwin da wasu masu suna Sunday Daniel da Obu Peters duka maza wadanda aka cafke da buhunan 387 da yakai kilo 4,000 a karamar hukumar Keffi a jihar.
Kwamandan Dechi Elisha Daɓid ya kara da cewa jimilar kudin muggan kayayyakin sun kai sama da naira miliyan 400 inda ya kuma yi amfani da damar ya sanar cewa a cikin watan na Mayun kadai hukumar ta aiwatar da gangamin wayar da kawunan al’umma ƙarƙashin wani shirin ta na musamman da ake kira WADA a Turance inda sama da mutane dubu 11 duka amfana da gangamin wayar da kawunan.
