Daga AISHA ASAS
Jarumar fina-finai Fati Washa ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin Biocare Nigeria, inda za ta zama jakadiyar tallar kayayyakinsu a faɗin Najeriya. Wannan haɗin gwiwa ya samo asali ne daga tasirinta a kafafen sada zumunta da amincewar da jama’a suka yi mata tate da shahara a matsayinta na jaruma a Masana’antar Kannywood.
Yarjejeniyar da aka sanya hannu a ranar 1 ga Yuni a Kaduna, ta haɗa da shirya tallace-tallace, fito wa a fina-finai masu faɗakarwa, da bayar da ilimi kan lafiya. “Ina alfahari da kasancewa jakadiya a wannan yunƙuri da zai taimaka wa lafiyar jama’a,” inji Fati Washa.
