Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWALa Haɗejia
Kungiyar Zakka da Waƙlaafi ta ƙasa (AZAWON) ta buƙaci gwamnatoci a matakin tarayya da jihohi da su yi amfani da tsarin Zakka da Waƙafi, domin magance matsalolin ƙuncin rayuwa da matsin tattalin arziki da ke addabar ƙasar nan.
Shugaban ƙungiyar Malam Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato, shi ya yi wannan kiran a yayin wani taron manema labarai da ƙungiyar ta kira a garin Haɗejia na Jihar Jigawa, a wani ɓangare na Babban Taron ƙasa da ƙungiyar ke gudanarwa karo na 4.
Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa, ƙididdigar da aka gudanar a shekarar 2015 ta bayyana cewa, Nijeriya na da damar samun isassun kuɗaɗe da za su ragewa al’umma raɗaɗin talauci.
“An kafa wannan ƙungiya ta AZAWON ne domin ɗa’a zuwa ga Allah, da kuma samarwa wannan ƙasa Nijeriya mafita daga irin yanayin da al’umma ta samu kanta a ciki, na barin dokokin Allah da kuma matsananci tashin hankali da talauci da muke fama da shi, da taɓarɓarewar al’amura. Muna ƙara sanar da al’umma cewa, dukkan bincike na duniya ya tabbatar da cewa, idan an fitar da Zakka kamar yadda Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi umarni, babu dalilin da zai sa jama’a su samu kansu cikin matsanancin talauci, da rashin abin da za su ci.’
Shugaban ya yi fatan dukkan masu ruwa da tsaki za su sa hannu cikin tsarin Zakka da Waƙafi, don al’ umma ta samu mafita, ƙasa ta samu cigaba.
