Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya mayar da martani kan furucin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, wanda ya ce ’yan Arewa su hakura da neman kujerar shugaban ƙasa a 2027, sai 2031 idan Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.
Manhaja ta ruwaito George Akume na cewa ’yan Arewa ’yan Jam’iyyar APC mai mulki da ke son neman shugabancin ƙasa su haƙura zuwa 2031, saboda a cewarsa, yanzu lokacin mulkin ’yan yankin Kudu ne, don haka su jira sai Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.
Ya kuma buƙaci Atiku, babban abokin hamayyan Tinubu a zaɓen 2023 daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya haƙura ya jira 2021.
Akume ya ci gaba da cewa idan Allah Ya nufi tsohon mataimakin shugaban ƙasan da zama shugaban ƙasa zai zama, ko da yana ɗan shekara 90 ne.
Amma a martanin Atiku, ya bayyana cewa zaɓin shugaban ƙasa abu ne da ke hannun ’yan Nijeriya zu zaɓi wanda suke so.
Ya bayyana kalaman Akume a matsayin rashin adalci, domin a halin yanzu, ’yan yankin Kudu sun mulki Nijeriya na tsawon shekara 17 ne — takwas a ƙarƙashin Obasanjo, biyar a hannun Jonathan da kuma huɗu a hannun Tinubu — idan aka kwatanta da ’yan Arewa da suka yi shekara 11, uku na Yar’Adua da takwas na Buhari.
Atiku ta hannun kakakinsa, Paul Ibe, ya ƙara da cewa hakan rashin adalci ne, yana mai bayyana cewa zaɓin shugaban ƙasa na hannun ’yan ƙasa yake, sai kuma irin shugabancin da gwamnati mai ci ta yi.
Paul Ibe ya ce, abin tambaya shi ne, “Shin me Gwamnatin Tinubu ta yi da ’yan Nijeriya za su ƙara zaɓen ta?”
