Yadda aka gudanar da taron bikin Kalankuwar Afirika KILAF AWARD 2024

Spread the love

(Ci gaba daga makon jiya)

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A farkon bude taron da misalin ƙarfe tara na safe ƙwararre kuma masani a kan harkar fim Yomi Olugbod shi ne ya gabatar da bita a kan aikin manajan shirya fim , wato ‘Production Manager’ inda ya yi dogon bayani a game da alaƙar manajan shirya fim da furodusa darakta da kuma jaruman fim.

Haka nan ya bada misalai da dama a kan tasirin managan shirya fim da kuma ingancin fim da kuma rashin ingancin sa.

Nasiru B Muhammad, shi ne ya yi sharshi tare da ƙarin bayani bayan Mista Yomi Olugbod ya kammala jawabin sa tare ƙarfafa wa mahalarta kan su mayar da hankali a game da abin da suke sauraro, yadda za su ci moriyar darasin da ake koyar da su.

Duk dai a wannan rana shi ma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta ƙasa Dakta Hussaini Shu’aibu, shi ya samu halartar wajen taron tare da gabatar da dan takaitaccen jawabi tare da nuna farin cikin sa da ya samu halartar wajen duk da ya zo a makare saboda wani aiki da ya taso masa a Legas, amma dai duk da haka ya yi ƙoƙari ya samu zuwa tare da rakiyar na ofishin shiyyar Arewa maso yamma. Ya yi tan alheri tare da ƙarfafa gwiwa ga mahalarta taron, inda ya ce yana da kyakkyawar fata a kan bunƙasar masana’antar finafinai ta Nijeriya, yadda shekaru masu zuwa za a ci gajiyar ta fiye da wannan lokacin.

Bayan ya kammala jawabin sa ne aka tafi hutun Sallah tare da cin abinci, wanda shi ma wani ɓangare ne mai muhimmanci a cikin tsarin taro.

Domin kuwa an samar da abincin Gargajiyar Afirika wanda ya dace da mutanen Afirika yadda duk inda mutum ya zo daga ƙasashen Afirika zai samu kalar abincin gargajiyar da yake buƙata. Hakan ya bayar da dama ga sanin abincin gargajiya kala-kala da ake amfani da su a ƙasashen Afrika.

An ci gaba da taron da misalin ƙarfe uku na rana tare da gabatar da Charlas Okwuowubu don ya gabatar da nasa jawabi.

Ya yi dogon bayani a game matakin tace fim bayan an kammala aikin sa wato ‘Editing Process’.

Haka nan ya yi bayani a kan yadda mai ɗaukar hoto zai yi amfani da fitila da kuma kalar hasken da ya kamata ya yi amfani da shi a kowanne sin da zai ɗauka,da yin amfani da waje da kuma lokacin da ya kamata.

 Ya dai kammala jawabin sa da misalin ƙarfe huɗu, aka tafi Sallah.

An kammala zaman taron na wannan rana da kallon wasu gajerun finafinai ne guda uku daya daga Najeriya mai suna ‘Tarnaki’ sai ‘Fatimah Zarah’ daga ƙasar Marocco da LiLa daga ƙasar Ruwanda. 

Daraktocin finafinan dai sun sha tambayoyi daga wajen mahalarta taron, har zuwa lokacin da aka rufe taron da misalin ƙarfe shida na yamma.

A rana ta biyar ta taron KILAF AWARD 24, an shiryawa mahalarta taron musamman baƙi da suka zo daga ciki da wajen ƙasar nan yawon buɗe Ido na nuna muhimman wuraren tarihi a cikin garin Kano.

Farko an kai baƙin Gidan Banhausa da ke titin Sokoto a Unguwar Nassarawa G R A, da kuma dayan da ke kusa da ma’aikatar ayyuka duk dai a cikin Unguwar Nassarawa, domin nuna kayan tarihi.

Haka nan an kai su gidan Makama wanda shi ma gidan adana abubuwan tarihi ne na ƙasar Hausa da ke kusa da Kofar Kudu. Sai kuma gidan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ll da shi ma wani ɓangare ne na abubuwan tarihi a garin Kano. Sannan aka kammala zagayen da zuwa Dutsen Dala da Gwauron Dutse suka hau suka ga abubuwan tarihi da na al’adun Kano da ƙasar Hausa.

Da ƙarfe huɗu na yamma kuma an dawo muhallin taron da ke Jami’ar Bayero inda aka ci gaba da nuna finafinan Afrika da suke nuna yare da muka al’adun Afirika, har zuwa ƙarfe shida na yamma.

Sai kuma ƙarfe takwas na dare aka shirya liyafar fitar da sunayen waɗanda suka shiga gasa suka zo matakin na biyun ƙarshe .

An dai shirya taron ne a Tahir Guest Palace da ke cikin Unguwar Nassarawa G R A. Kuma an samu muhimman mutane da suka halarci taron.

A rana ta ƙarshe wato Asabar 30 ga Nuwamba ne aka kawo ƙarshen taron da bayyana sunayen jarumai da kuma finafinan da suka yi nasara a gasar ta bana.

Taron dai an shirya shi a babban ɗakin taro na Gidan Gwamnatin Jihar Kano, wanda ya samu manyan baƙi daga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kano wanda Kwamishinayar Ma’aikatar Al’adu da yawon buɗe Ido Hajiya Ladidi Ibrahim Garko ta wakilci Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif, sai kuma Hajiya Kaltume Gana ta wakilci Ministar Al’adu Hannaru Musawa, da dai sauran manyan baƙi.

An dai bayyana Yakubu Muhammad a matsayin Gwarzon Jarumi na gasar KILAF AWARD 2024 wanda ya ci gasar da fim ɗin ‘KAKA’, sai kuma Gwarzuwar Jaruma Nice Githinji da ta yi nasara da fim din ‘The Coller’. Da dai sauran jarumai da finafinai da suka yi nasara a gasar

An yi taron bikin na bana an kammala lafiya, kuma tuni jama’ar da suka halarci taron kowa ya koma garin su. Sai kuma Allah ya kaimu shekara mai zuwa ga mai yawan rai.i

By ukarofi