Fitowata daga kurkuku sabon babi ne a rayuwata – Faruk Lawan

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Dan Majalisar Wakilai, Hon. Farouk Lawan ya shaƙi iskar ’yanci daga gidan yari na Kuje bayan ya kammala zamansa, inda ya bayyana ficewar a matsayin wani sabon babi a rayuwarsa.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, Adamu Duza, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce: “Eh, an sake shi ne bayan ya kammala zaman da aka tanke masa.”

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Lawan ya gode wa Allah da samun kansa, wanda ya ce, ya zama farkon wani sabon babi a rayuwarsa.

Ya ce, “na gode wa Allah Ta’ala. Alhamdulillah. Alhamdulillah. Alhamdulillah. A yau ne wani sabon babi na rayuwata ya fara a lokacin da na fito daga kurkukun Kuje. Ina godiya ga Allah (SWT) da ya saka ni cikin wannan jarrabawa.

“Godiyata tana da yawa; Ina raye kuma Ina cikin ƙoshin lafiya kuma Ina jin daɗin kasancewa tare da iyalina da abokan arziki. Ba na ɗaukar hakan da wasa.

“Ina godiya ga iyalai da abokaina da suka ba ni goyon baya a cikin wannan mawuyacin hali na rayuwata. Allah Ya saka muku da alheri.”

Kafin halin da ya shiga, Lawan yana ɗaya daga cikin ’yan majalisar da ke da tasiri a Majalisar Dokokin Nijeriya kuma ya kasance gwarzo na wasu, kamar yadda a zahiri ya kasance yana da hannu a cikin naɗin dukkanin shugabannin majalisar kafin shekarar 2015.

Tsohon ɗan majalisar na PDP, wanda shi ne shugaban ƙungiyar “Integrity Group” a majalisar, wanda ya kitsa tsige tsohuwar kakakin majalisar a lokacin, Patricia Etteh, an zaɓe shi a majalisar wakilai sau huɗu a 1999, 2003, 2007 da kuma a 2011.

Sakamakon cire tallafin man fetur a watan Janairun 2012 wanda ya haifar da zanga-zanga da yajin aiki a faɗin ƙasar, Lawan ya jagoranci wani bincike na Majalisar Wakilai kan tsarin tallafin mai wanda aka yi ta yin kiyasin badaƙalar dala biliyan 6.8.

Bankaɗar Faruk Lawan ua jagoranta ta haifar da abin kunya ga tsohuwar gwamnatin Shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan, lamarin da ya sanya ake ganin gwamnatin lokacin ta sako tsohon ɗan majalisar a gaba.

A watan Fabrairu, 2013, an zargi Lawan da neman rashawar Dala miliyan uku daga fitaccen ɗan kasuwa, Femi Otedola, don cire kamfaninsa na Zenon daga cikin jerin kamfanonin mai da ake zargi da hannu a badaƙalar tallafin man fetur da ta girgiza al’ummar ƙasar shekaru da suka gabata.

Daga baya an same shi da laifin neman rashawa da kuma karɓar cin hancin Dala 500,000 daga hannun ɗan kasuwa Femi Otedola, shugaban kamfanin mai da iskar gas na Zenon, duk da kiraye-kirayen da aka riƙa yi a binciki shi ma ɗan kasuwar.

Sai dai a watan Yunin 2021 ne aka yanke wa Lawan hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari. Sai dai kotun ɗaukaka ƙara ta rage masa hukuncin zuwa shekaru biyar, saboda wanke shi daga laifin da aka zarge shi na neman a ba shi cin hanci, hukuncin da Kotun ƙoli ta tabbatar a watan Janairun 2024.

Tsohon ɗan majalisar tarayya, wanda ya wakilci mazaɓar Bagwai da Shanono daga Jihar Kano a Majalisar Wakilai, duk da cewa, kotu ta kama shi da laifin, amma da yawa na kallon lamarin a matsayin mai cike da siyasa da kuma ramuwar gayyar siyasa.

By ukarofi