Mafi ƙarancin albashi: Gwamnan Kebbi ya amince da biyan N75,000 ga ma’aikata

Spread the love

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi 

Gwamnan Jihar Kebbi Malam Nasir Idris ƙauran Gwandu ya bi sahun waɗansu daga cikin gwamnoni da suka amince da biyan mafi ƙarancin albashi ka da ya kasa Naira 70,000 ga ma’aikatan jihohinsu tare da ƙananan hukumomi.

Ranar Larabar da ta gabata ne gwamnan na jihar Kebbi ya amince da biyan Naira 75,000 ga ma’aikatan jiha da ƙananan hukumomi zuwa malamai, inda ya umarci kwamishinan kuɗi da babban akawun kuɗi na jihar da su tabbatar da an biya sabon mafi ƙarancin albashin a cikin kwanaki biyu daga Laraba zuwa yau Juma’a. 

Gwamnan ya bayyana cewa ya amince da sabon mafi ƙarancin albashin ne tare da sanya masa hannu a matsayin doka a ranar Laraba 23 ga Oktoba, 2024 a gaban gamayyar ƙungiyar ƙwadago na jihar Kebbi saboda haka ya zama lallai a biya kowane ma’aikaci.

Ya kuma yaba wa gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na reshen jihar Kebbi bisa irin goyon bayan da suke bai wa wannan gwamantin da kuma fahimta tun a lokacin da aka rantsar da ita wanda ya ce ba ƙaramin ƙwarin gwiwa ya ke ba shi ba.

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC Joe Ajero da yake nasa jawabin a wurin taron, ya yaba wa Gwamna Nasir Idris ƙauran Gwandu bisa irin ayyukan cigaban al’umma da yake gudanarwa a faɗin Jihar ta Kebbi duk da cewar jihar tana fuskantar ƙarancin hanyoyin samun kuɗin shiga.

Ya bayyana irin waɗannan ayyukan cigaban da Maigirma Gwamna Nasir Idris ya gudanar a ɓangarori daban-daban da suka haɗa gyarawa da haskaka titunan babban birnin jiha, ginawa da gyara makarantu da asibitoci, samar da takin zamani ga manoma kyauta, injinan ban ruwa da kuma inganta jin daɗi da walwalar ma’aikatan jiha gaskiya ba kowane jiha da ke da ƙarancin kuɗin shiga ke iya yi ba.

Shugaban na NLC ya jinjinawa gwamna wajen biyan albashin ma’aikata akan kari, da kuɗin ajiye aiki na giratuti da kuma na fansho.

By ukarofi