Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Hukumar jin daɗin Alhazzai ta Kebbi ta yi kira ga maniyyata aikin hajji na shekarar 2025 mai zuwa da su soma kai kuɗin ajiya na adashin gata da aƙalla kada ya yi ƙasa da Naira milliyan shida a matsayin kuɗin ajiya na farko.
Haka-zalika kuma ana sa ran kowane maniyyaci zai biya sauran ragowar kuɗin kujerarsa daga nan zuwa watan Nuwamba mai zuwa da za su iya kai naira miliyan biyu da dubu ɗari huɗu.
Da ya ke bayani, shugaban hukumar jin dadin alhazan Alhaji Musa Yaro (Enabo) ya ce wannan shi zai bai wa hukumar tabbacin maniyyaci ya shirya har wa ya shi ne zai bai wa hukumar damar kammala ayyukanta cikin lokaci.
Ya ƙara da cewa sanadiyyar kyakykyawan tsari da hukumar ta yi a shekarar da ta gabata shi ne ya sa ba a samu wata matsala ko ƙorafe-ƙorafe ba kamar yadda ake samu a baya.
