Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu
Hukumar Zartaswar Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gashuwa a Jihar Yobe (FUGA) a, taronta na 44 a ranar Jummu’a, a ƙarƙashin shugabar jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri, ta amince da naɗin Dokta Ibrahim Ahmed Jajere da Dokta Mohammed Attai Yakubu a matsayin Mataimakan Shugabar Jami’ar; na ƙwararru da na sha’anin gudanarwa.
A cikin wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar, Malam Adamu Saleh ya fitar ta ce, Hukumar Zartaswar ta amince da naɗin mataimakan shugabar jami’ar guda biyu ne a ƙarƙashin doka Sashe na 4 na dokokin Jami’o’i mai lamba 11 na shekarar 1993, wanda ya bai wa Hukumar gudanarwar Jami’ar ƙarfin ikon naɗin mataimakan shugabar jami’ar biyu.
Dr Ibrahim Ahmed Jajere, malami (Reader) ne a tsangayar nazarin Kasa kuma Darakta ne a Cibiyar Nazarin Bunƙasa Bishiyar Karo, kafin daga bisani aka zaɓe shi matsayin mataimakin Shugabar Jami’ar (Academic), yayin da Dr. Mohammed Attai Yakubu, shi ma malami ne (Reader) a tsangayar koyon harshen Turanci da kuma Daraktan Al’amurran Cigaba, wanda daga bisani aka zaɓi’e shi a matsayin Mataimakin Shugabar Jami’ar kan harkokin gudanarwa (Administration).
A jawabinsu jim kaɗan da naɗin, Dr. Mohammed Attai Yakubu, wanda ya yi magana a madadin su biyu, ya fara da gode wa shugabar jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri, tare da mambobin Hukumar Zartaswar jami’ar bisa ganin cancantar su wajen wannan naɗin, inda ya bayar da tabbacin za su yi aiki tukuru wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
A hannu guda, Adamu Saleh ya ƙara da cewa, Hukumar Kula da Al’amarran Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), ta amincewa jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gashuwa (FUGA) ƙarin wasu kwasa-kwasai don fara karatun Digiri na biyu (M.A) da na uku (Ph.D), waɗanda za su fara a zangon karatu na 2023/2024 a jami’ar.
Haka zalika kuma, ya kara da cewa, hakan ya zo ne sakamakon nasarar aikin tantance ma’aikata tare da tsare-tsaren jami’ar wanda Hukumar Kula da Jami’o’i (NUC) ta gudanar a cikin watan Yulin 2023. Sabbin kwasa-kwasan sun haɗa da Digiri na biyu (M.A) da na uku (Ph.D) a fannin Ilimin Addinin Musulunci (Islamic Studies) sai Digiri na biyu (M.Sc) da na uku (Ph.D) Accounting, Digiri na biyu (M.Sc) da na uku (Ph.D) Taxation.
Sauran su ne Digiri na biyu (M.Sc) da na uku (Ph.D) Economics, da fannin Geographic Information System, a Digiri na biyu (M.Sc) da na uku (Ph.D) Geography, Digiri na biyu (M.Sc, MPA) da na uku (Ph.D) Public Administration. Digiri na biyu (M.Sc) da na uku (Ph.D) Chemistry, saiw Digiri na biyu (M.Sc.) da na uku (Ph.D) Mathematics.
Har wa yau, NUC ta amince wa jami’ar ƙarin wasu kwasa-kwasai a matakin karatun Digiri na farko; B.Sc. Microbiology, B.Ed Guidance and Counseling, Educational Foundation, B.Sc. Ed. BSc. Ed. Primary Education, B.Sc Ed. Agricultural Science. B.Sc. Ed. Mathematics, B.Sc. Ed. Physics, B.Sc. Ed. Chemistry, B.Sc. Ed Biology, B. Library and information Science, (BLIS) B. Ed English Language.