Fusatattun matasa sun cinna wa jami’in NDLEA wuta da ransa

Spread the love

A ranar Juma’a, 14 ga Fabrairu, wani jami’in Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA), mai suna Aliyu Imran, ya rasa ransa a garin Gadan-Gayan da ke ƙaramar Hukumar Igabi, a Jihar Kaduna.

A cewar rahotanni, an banka wa jami’in NDLEA, Aliyu Imran, wuta da ransa, har ya ƙone ƙurmus bayan wani hatsari da ya haddasa mutuwar mutane uku.

Hatsarin ya faru ne yayin da shi da abokan aikinsa ke bin wata motar masu laifi, wacce ta murƙushe mutane yayin ƙoƙarin tserewa.

Bayan afkuwar hatsarin, Imran ya yi ƙoƙarin kwantar da hankalin jama’a, amma fusatattun mutane a wajen suka kai masa hari, inda suka soka masa wuƙa.

Daga nan, wani zan sanda ya kai shi asibiti, amma matasan suka bi shi har can, suka janye shi daga asibitin, tare da ƙona shi da ransa.

Iyalansa sun zargi NDLEA da rashin ɗaukar matakin da ya dace bayan faruwar lamarin, suna mai cewa ba a je masu ta’aziyya ko a yi batun biyansu diyya ba.

An ruwaito cewa kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya musanta zargin, yana mai cewa hukumar ta tuntuɓi iyalan mamacin.

Hakazalika, Femi Babafemi ya shaida cewa NDLEA ta dakatar da kwamandan da ya jagoranci aikin domin gudanar da bincike

By ukarofi