Haɗarin tankar mai kan titin Lapi-Bida ya kashe mutum 14

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Wani hatsarin tankar mai ya yi sanadin mutuwar mutane 14 tare da jikkata wasu guda shida a kan titin Lapai-Agaie-Bida a jihar Neja. Kwamandan sashen hukumar FRSC na jihar, Kumar Tsukwam, ya tabbatar da faruwar wannan mummunan hatsari, yana mai danganta shi da gudu fiye da kima da ganganci.

Hatsarin ya afku ne da misalin ƙarfe 10:59 na safe a ranar Asabar, 22 ga Fabrairu, 2025, tsakanin yankunan Kusobogi da Nami. Wata motar Toyota Hiace da ke tafiya daga Minna zuwa Agaie ta yi karo da tankar DAF da ke kan hanyarta daga Legas zuwa Kaduna, sakamakon yunƙurin wucewa ba tare da kulawa ba.

Sakamakon haɗarin, mutum 14 suka rasu nan take, ciki har da mata biyar, yaro namiji ɗaya, da maza takwas. Haka kuma, maza guda shida sun samu munanan raunuka kuma an garzaya da su asibitin Lapai don samun kulawar gaggawa. Gawarwakin waɗanda suka mutu an ajiye su a ɗakin ajiye gawa.

Kwamandan FRSC ya gargaɗi direbobi da su kiyaye dokokin hanya, su guji tuƙin ganganci, tare da tabbatar da lafiyar motocinsu don kauce wa irin waɗannan haɗurran da ke ci gaba da yin ɓarna.

By ukarofi