Ministan Tsaro ya buƙaci haɗin kan Jama’a wajen samun cigaba a Jihar Jigawa

Spread the love

Daga UMAR MAJERE a Dutse

Minista Badaru Abubakar ya buƙaci haɗin kan al,ummar Jihar Jigawa wajen wani taro a ƙaramar hukumar Birnin kudu a ranar Lahadi.

Tsohon Gwamnan yace jami,an tsaron Nijeriya suna matuƙar ƙoƙari wajen tabbatar da tsaro a jihohin Katsina ,zamfara,Sokoto, kaduna da Jihar Neja .

Ministan yace an sami raguwar yawaitar aiyukan ta’addanci a yankunan waɗannan jihohi da aka anbaci sunayansu. Ya kuma bai wa yan Nijeriya tabbacin cewar za,a Sami zaman lafiya a dukkan yankunan da ake fama da yaɗuwar ayyukan ta’addanci da suka jima suna damun al,ummar yankunan da satar mutane ,kashewa da asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.

Ya kuma yiwa ƴan Nijeriya albishirin cewar nan bada jimawa ba za a sami sassauci a kan hauhawar farashin kayan abinci daya jima yana damun al,ummar Nijeriya.

Ministan ya cigaba da cewar komai zai yi sauƙi domin farashin kayan abinci zai sauka, jama,a za su sami sassaucin kamar yadda suke kyautata zato.

Shima da yake nasa jawabin a wajen taron Alh Isah Gerawa ya gargaɗi masu adawa su taka a sannu wajan rura wutar rikici a cikin jam’iyyar APC domin su a yanzu babu sauran wata rigima a cikin jam’iyyar.

Ya ƙara da cewa duk wasu masu kutungwila da suke ƙoƙarin haifar da fitina a cikin tafiyarsu ta APC ƙarƙashin wannan tafiya za su ji kunya.

By ukarofi