Ganduje ya bai wa makaho aiki saboda bajintarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa Ɗahuru Abdulhamid Idris wanda makaho ne, aikin koyarwa a gwamnatin jihar.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Labarai na gwamnatin jihar, Abba Anwar ya fitar a ranar Lahadi.

Kafin wannan lokaci, Ɗahuru ya kasance yana aikin koyarwa na sa-kai ba tare da ana biyansa wani albashi ba.

Sanarwar ta ce bayan da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammadu Sanusi Kiru, ya jagoranci Ɗahuru zuwa gaban Ganduje ne, a nan Ganduje ya bada umarnin a ɗauke shi aiki sannan a tura shi Makarantar Nakasassu da ke Tudun Maliki don ya ci gaba koyarwa.

Yayin ganawar tasu, Ganduje ya yaba wa ƙoƙarin Ɗahuru musamman ma ganin yadda bai bari lalurar makanta ta hana shi bada tasa gudunmawa ga cigaban fannin ilimin jihar ba.

Bisa wannan dalili ne Gwamna Ganduje ya ce, “Lallai ka taki matakin da ya dace a rayuwarka. Gwamnatin jihar Kano ta ba ka aikin koyarwa. Kuma na umarci Kwamishinan Ilimi da a tura ka zuwa makarantar masu fama da nakasa da ke Tudun Maliki.”

Yanzu dai ya tabbata cewa, Ɗahuru Andulhami Idiris ya zama ma’aikacin gwamnatin jihar Kano inda ake sa ran shi ma ya riƙa cin albashi kamar sauran ma’aikatan jihar duk ƙarshen wata.