Rashin amfana da mulkin Buhari ya sa ‘yan Arewa ƙin jinin tsarin karɓa-karɓa – Na’Abba

Daga BASHIR ISAH

Tsohon shugaban Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Ghali Umar Na’Abba, ya bayyana cewa galibin ‘yan Arewa na kallon mulkin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin salwantar da muhimmiyar damar da ta samu ga yankinsu.

Na’Abba ya yi wannan furuci ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a cikin shirin siyasa a tashar talabijin ɗin Daily Trust, inda ya ce da daman ‘yan Arewa na ƙin tsarin mulki na karɓa-karɓa ne ba don komai ba sai don ganin cewa babu wani amfani da suka samu a mulkin Buhari.

Tsohon shugaban majalisar ya ce, Buhari mutum ne mai tsattsauran ra’ayi sannan yana mulkin ƙasa ba tare da tuntuɓa da neman shawara yadda ya kamata ba.

Ya ce, “Lamarin ba wai yaƙi ne tsakanin ‘yan Arewa da ‘yan Kudu ba, amma a kowace zamantake lokaci zuwa lokaci za a riƙa samun ‘yan matsaloli. Waɗannan matsaloli kuwa na aukuwa ne saboda wasu dalilai.

“Fahimtar da ake da ita a halin yanzu kan cewa Buhari ba ya son ‘yan Kudu ya zama abu bayyananne. Ina ganin ba ya tafiyar da ƙasar nan ta yadda sha’anin siyasa zai samu tagomashi, hatta a Arewa ana ƙorafe-ƙorafe a kansa.

“Bai kamata ka mulki ƙasa bisa tsattsauran ra’ayi irin naka ba, sannan wannan ra’ayi naka bai shafi jama’a ba. Idan kuwa ra’ayin ya shafi jama’a da walwalarsu da kuma ra’ayiyinsu, ina ganin hakan daidai ne.

“Al’ummar Kudu sun yarda da cewa Buhari na nuna ƙabilanci, ba zai iya riƙe ƙasar nan ba. Akwai wanda ya faɗa mini cewa ko gidansa ma Buhari ba zai iya kulawa da shi ba, ta yaya zai iya riƙe ƙasa ɗungurungun?

“Wannan tsari na karɓa-karɓa, komai yawan shugabanci da wata shiyya ta samu hakan ba zai taɓa wadatar da kowa ba. Alal misali, yau a tsakanin ‘yan Arewa batun cewa shugabancin ƙasa ya koma wata shiyya ba son shi suke ba saboda da yawansu na jin cewa mulkin wannan shugaba mai ci wata muhimmiyar dama ce aka salwantar babu abin da suka amfana da shi.

“Don haka me ma zai sa wani ya fito yana yi musu batun karɓa-karɓa? Alhali sun kwana da sanin cewa suna da ƙarfin da za su fito su sake zaɓen wani.

“Tun da ya yi ra’ayin cewa zai iya komai shi kaɗai babu ruwansa da tuntuɓa da neman shawara. Ba wai ana zama shugaba ba ne saboda ka zama kai kaɗai gayya ko don ƙarfin hikima. Babu wanda ke da wannan.”

Na’Abba ya ce domin ƙasa ta inganta ta yadda ‘yan ƙasa za su sakata su wala, dole a maida hankali wajen gina muhimman cibiyoyi amma ba gina masu ƙarfin iko ba.