Garkuwa ya yi godiya ga jama’ar Abba Na Shehu

Daga HABU DAN SARKI a Jos

Mataimakin Shugaban ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, Kabiru Sani Muhammad Garkuwa, ya yi godiya ga jama’ar mazaɓarsa ta Abba Na Shehu, domin gagarumin goyon bayan da suka bashi, a lokacin zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a Jihar Filato cikin watan Oktoba da ya gabata, wanda ya bai wa Jam’iyyar PDP nasarar kafa gwamnati a ƙaramar hukumar.

Mataimakin Shugaban ƙaramar Hukumar, ya yi wannan godiyar ne a yayin wani taron Muhadara da ƙungiyar Raya Anguwar Abba Na Shehu ta shirya albarkacin azumin watan Ramadan, wanda Kabiru Garkuwa ya kasance shugaban Kwamitin Tuntuɓa da Tsare-tsare.

Ya ce, babu shakka al’ummarsa ta Abba Na Shehu sun fitar da shi kunya kuma sun nuna cewa shi ɗansu ne da suke alfahari da shi.

“Duk da nasarar da Jam’iyyar mu ta samu a wannan ƙaramar Hukuma, da a ce ban ci zaɓen mazaɓata ba to, yana nufin ban ci zaɓe ba. Kuma wannan nasara ta samu ne da goyon bayan ku.”

Ya ce, zai cigaba da kasancewa mai biyayya ga al’ummar wannan mazaɓa tare da yin duk abin da ya kamata bisa tanadin doka, don ganin mata da matasa da duk wani wanda ya cancanta ya samu abin da ya dace na romon dimukraɗiyya.

Shugaban ƙungiyar Raya Al’ummar Abba Na Shehu, Alhaji Auwal Al-Mansur ya bayyana cewa, suna alfahari da irin gudunmawar da yake bayarwa a jagorancin ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, kuma za su cigaba da sa’idanu don ganin ya yi nasara kan dukkan muradun da ya sa a gaba, tare da ba shi shawarwarin da suka kamata, a matsayin su na shugabanni kuma masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar.