Gaskiya ba ta ɓuya…

Daga IBRAHIM YAYA

Bisa ga dukkan alamu, ci gaban da ƙasar Sin ta samu a fannoni daban-daban da irin gudummawar da take bayarwa ga ci gaban zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunƙasuwar tattalin arziki da sauran sassan rayuwa a faɗin duniya, ya damu wasu ƙasashe, waɗanda suke kallo kansu a matsayin jagororin duniya.

Wannan ya sa daga lokaci zuwa lokaci, irin waɗannan ƙasashe suke neman ɓata sunan ƙasar Sin ko salon jagorancin ƙasar da al’ummar ƙasar suka yi na’am da shi ko wani tsari da ta gabatar da nufin inganta rayuwar daukacin bil-Adama, kamar shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya da makamantansu.

A wasu lokuta ma, irin waɗannan ƙasashe dake adawa da ci gaban ƙasar Sin, kan fake da batutuwan tsarin demokuraɗiyya da haƙƙin dan-Adam wajen neman tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasar Sin.

Sai dai, yanzu kan mage ya waye, ƙasashe da dama sun fahimci makircin ƙasashen yamma, inda suka fara dawowa daga rakiyarsu, domin kada su zuba musu ƙasa a cikin kununsu. Ta hanyar lalata shirye-shirye masu fa’ida da Sin din ta gabatar, da galibin ƙasashe masu tasowa suka amfana da su.

Na baya-bayan shi ne ministan kuɗi na ƙasar Bangladesh, inda ya fito ƙarara ya soki wasu rahotannin ƙarya da kafofin yaɗa labaran Burtaniya suka yi kan ƙasar Sin, matakin dake nuna irin cikakkiyar amincewa da juna dake tsakanin Sin da Bangladesh, kuma hakan ya tabbatar da abin da ƙasar Sin ta sha faɗa cewa, gaskiya ba ta buya, kuma komin daɗewa, adalci zai bayyana kansa.

A matsayinta na ƙasa mai tasowa mafi girma a duniya, har kullum ƙasar Sin tana tare da sauran ƙasashe masu tasowa, kana tana gudanar da hadin gwiwar “ziri dayya da hanya ɗaya” da masu neman hana ruwa gudu ke neman batawa bisa tsarin tuntubar juna, da gudummawar haɗin gwiwa, da samun moriyar juna.

Bayanai sun tabbatar da cewa, batun “tarkon bashi na ƙasar Sin” a zahiri wani “tarkon tattaunawa ne” da wasu mutane masu mugun nufi suka ƙirƙira, don kawo cikas da kuma gurgunta haɗin gwiwar moriyar juna tsakanin Sin da sauran ƙasashe masu tasowa. Amma yanzu kan gaskiya ta bayyana, babu wanda zai rudi ƙasashen da suka amfana da tallafi da goyon bayan da ƙasar Sin ke baiwa abokanta ƙasashe masu tasowa.

Sanin kowa ne cewa, shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya, ta samu gagarumin goyon baya da shigar ƙasashe masu tasowa da dama. Haka kuma haɗin gwiwar ta haifar da kyakkyawan sakamako, ta kuma samar da fa’ida ta haƙiƙa ga jama’ar dukkan ƙasashe.

Don haka, duk wasu kalamai marasa kyau da ke neman bata sunan shawarar da haɗin gwiwar Sin da sauran ƙasashe masu tasowa, da masu neman mayar da hannu agogo baya ke ƙirƙira, ƙaiƙayi ne zai koma kan mashekiya.

Fassarawar Ibrahim Yaya