Wang Yi zai karɓi baƙuncin taron masu gudanarwa game da haɗin gwiwar Sin da Afirka

Daga CMG HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, zai jagoranci taron ƙolin masu tsara aiwatar da ayyukan da suka biyo bayan taron ministocin dandalin tattaunawa kan haɗin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) gobe Alhamis 18 ga watan Agustan da muke ciki.

Mambobin hukumar zartaswar taron kolin ƙungiyar tarayyar Afirka, da ƙasashen Senegal, da Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo, da Libya, da Angola da wakilan ministocin ƙasashen Habasha, da Masar da Afirka ta Kudu, wato tsoffin shugabannin Afirka na dandalin FOCAC, da wakilan hukumar gudanarwar ƙungiyar tarayyar Afirka, za su halarci taron.

Fassarawar Ibrahim