Gaskiyar zance game da auren biloniya, Nwoko, da ‘yar wasan barkwanci, Emmanuella

Daga AISHA ASAS

A cikin satin da ya gabata ne kafafen sada zumunta suka karaɗe da zancen auren fitaccen mai kuɗin nan na Kudu, Ned Nwoko da kuma sharararriyar ‘yar wasan barkwanci Emmanuella Samuel, inda ake yaɗa cewar har an masu baiko, ma’ana Ned ya nemi iznin aurenta har wurin iyayenta.

Wannan zancen ya jawo ce-ce-kuce tsakanin masoyan Emmanuella da ke ganin rashin dacewar su da kuma masu kallon iyalin biloniyan wanda a kwanan nan aka haifa ma shi jinjiri, wanda jaruma Regina Daniels ta haifa masa. Sai dai an kasa samun wanda zai fayyace sahihancin wannan zance, don haka labarin ya ɗauki ɗan lokaci yana yawo, kafin shi wanda lamarin ya shafa ya bayyana gaskiyar zancen.

Nwoko ya ƙaryata zancen zuwa wurin iyayen Emmanuella neman aurenta da ma zancen na aure gabaɗaya. Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram, yayin da ya ke amsa tambayoyi daga mabiyansa, inda ya bayyana lamarin a matsayin tatsuniya.

A lokacin da yake amsa tambayar ɗaya daga cikin mabiyansa a shafin mai amfani da suna don.makas.165, wanda ya tambaye shi ko yana da niyyar auren matashiyar Emmanuella? Ya amsa shi da cewa, “ina da kyawawan mata.”

Jim kaɗan bayan amsa wannan tambayar, wata mabiyar tasa mai amfani da @jennifereverest24, ta sake zafafa zancen da tata tambayar inda ta ce, “na ji an ce kai da Emmanuella za ku yi aure. Ko zancen gaskiya ne?” Shi kuwa ya mayar mata da amsa kamar haka, “labarin ƙarya ne.”