
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon mataimaki na musamman akan harkokin Arewa ga tsohon gwamnan Jihar Legas (Lateef Jakande), Kwamared Salihu Ɗantata Mahmud ya yi alla-wadai da wasiƙar gayyatar Mai Martaba Sarkin Kano Sanusi Muhammad na biyu da ƴan sanda suka yi masa zuwa Abuja.
Salihu ya yi bayyana hakan ne a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai, inda ya ce Sufeton Janar Egbetokun bai daraja masarautun Arewa ba.
Ya ce, shin zai iya gayyatar Alake na Egba a Abeokuta ko Awujale na Ijebu Ode don zuwa yin bincike?
“Ina shawarar babban Sufeto Janar akan ya bar kaza a gashinta, saboda wanna neman fitina ne. Idan neman bayanai ya ke daga wurin Sanusi, mene ne anfanin runduna ta ɗaya, wato zone 1 ta Kano da ke da AIG KO kuma Kwamishinan ƴan sanda na Kano?”
Ya kuma ce, matuƙar ya amince da zuwan Sarki Sanusi, to wata rana ana iya yi wa sarkin musulumi haka.
Saboda haka, ya yi kira ga dattawan Arewa da su haɗa kai su hana wanna cin mutunci da aka shiriya.
