
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin kamo maharan da suka kashe mutane a wasu ƙauyuka dake Jihar Filato da kuma hukunta su kamar yadda dokar ta tanadar.
Ya kuma jajenta wa iyalan waɗanda aka kashe a yankunan Ruwi, Hurti da Tadai dake Ƙaramar Hukumar Ɓokkos da kuma wasu daga ƙauyukan Manguna da Dafo, inda nan ma mahara sun kashe mutane da ɗaiɗaita dukiyoyin al’umma.
Haka kuma ya jajenta wa Gwamantin jihar ƙarƙarshin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang, ya na mai kira ga al’umma da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai a ƙoƙarinsu na kamo waɗanda ke da hannu a laifin.
Bugu da ƙari, ya tabbatar wa gwamnan cigaba da ba shi goyon baya da tallafa masa wajen kawo ƙarshen fitintinun da ake fama da su a jihar.
Shugaba Tinubu ya umarci Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa da ta haɗa hannu da hukumomin tsaro na jihar wajen kula da waɗanda iftila’in ya afka masu.
