Gidauniyar Fasaudat ta tallafa wa ‘yan gudun hijra a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

‘Yan gudun hijira dake zaune a Ramen Kura a jihar Sakkwato sun samu tallafin abinci da tufafin sawa daga Gidauniyar tallafa wa marasa ƙarfi daga gidauniyar ta Fasaudat.

Baya ga kayan abinci haka ma gidauniyar ta tallafa wa yaran ‘yan gudun hijirar da tufafin sawa.

Da take ƙaddamar da tallafin shugabar gidauniyar Hajiya Fatima Ahmed Maigari ta yi kira ga matan ‘yan gudun hijira da su kula da karatu da kuma tarbiyyar ‘ya’yansu.

“Ina mai kira a gareku da kada ku dubi halin da kuke cike, ku yi amfani da damar ku wajen sauke nauyin da Allah ya ɗora maku ta ilmantar da kuma tarbiyyantar da yaran ku,” inji ta.

Fatima Maigari ta jajanta musu akan halin da suka tsinci kansu, inda ta roƙi Allah ya gwada musu ranar da za su koma garuruwansu.

Haka ma ta yi alƙawarin saka ‘ya’yansu makarantar boko da kuma koyawa wasu daga ciki sana’o’i.

A lokacin bayar da tallafin Dr. Tambari Waziri, Ammar Sidi Attahiru da kuma Abubakar Mailato sun gabatar da saƙon fatan alkhairi.

Ita ma da take jawabi, shugabar matan ‘yan gudun hijira Malama Binta Abubakar ta gode wa gidauniyar da kuma wadda ta assasa, inda ta roƙi Allah ya saka mata da alkhairi.

Galibin ‘yan gudun hijirar dai sun fito ne daga Sabon Birni, Isa, Goronyo, Rabah da kuma jihar Borno.