Wata gobara ta tashi a daren ranar Asabar a shahararriyar kasuwar Kantin-Kwari da ke Kano.
Kayayyaki da kadarori na miliyoyin a ka kiyasta asarar su a wannan mummunar gobarar kamar yadda Jaridar Blueprint ta rawaito.
Jaridar Blueprint ta cigaba da rawaito yadda yan kasuwa su ka fito su na fafatawa da wutar domin ganin sun rage asarar da su ka tafka.
Ɗaya daga cikin ’yan kasuwar , Alhaji Hamisu Sabo, wanda ya zanta da Blueprint ya bayyana abin da ya faru da shi.
Ya ce, “Wani ya kira ni da misalin karfe 7:30 na yamma a yau Asabar ya na sanar da ni cewa gobara ta tashi a kasuwa.
Da isa na wurin, shaguna biyu ne kawai su ka ƙone. Domin a yanzu haka muna ƙoƙarin gano musabbabin gobarar ne.
Har yanzu dai hukumomi ba su ce komai ba kan lamarin a daidai lokacin da ake haɗa wannan rahoto.
