Gobe ƙungiyar ANA reshen Kano za ta gudanar da taron bita

Ƙungiyar Marubuta ta Ƙasa Reshen Jihar Kano (ANA Kano) za ta gudanar da taron karatunta na Hausa na watan Satumba 2021, inda za a baje kolin fasahar adabi daga mambobinta kamar yadda ta saba yi a duk Lahadin farko na kowane wata.

Ƙungiyar ta ce taron wannan karon zai ƙunshi har da yi wa masu sha’awar rubutun Hausa bita a kan yadda ake rubutu da harshen Hausa bisa ƙa’idojin harshen.

Malam Yusuf Salisu Sani wanda masanin harshen Hausa ne daga Kwalejin Shari’a Da Ilimin Addinin Musulunci Ta Malam Aminu Kano, shi ne wanda zai jagoranci bitar kan ƙa’idojin rubutun Hausa.

Sanarwar da ta fito ta hannun Mataimakiyar Shugaban ANA Kano, Maimuna Sani Beli, ta nuna bitar sabon tsari ne da ƙungiyar ta ƙirƙiro don kawo bunƙasa a rayuwar jama’a.

Haka nan, sanarwar ta ce ƙungiyar ta shirya tsaf domin gudanar da wannan muhimmin taro, don haka ta ce tana gayyatar kowa zuwa wajen taron. Tare da cewa, ana maraba da rubutattun waƙoƙi da ƙagaggun gajerun labarai da ma wasannin kwaikwayo daga mambobinta.

Taron zai gudana ne gobe Lahadi a Ɗ’akin Taron American Space da ke Babban Ɗakin Karatu na Murtala Muhammad, titin Ahmadu Bello Way, Kano a ƙarƙashin jagorancin Dr. Isa Muhammad Inuwa daga Jami’ar Bayero, Kano.