Zaɓen Ƙananan Hukumomi: El-Rufai ya koka kan rashin fitowar jama’a zuwa wajen zaɓe

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nuna damuwarsa kan rashin fitowar jama’a don kaɗa ƙuri’a yayin zaɓen ƙanan hukumomin jihar a yau Asabar.

Gwamnan ya bayyana damuwarsa ne jim kaɗan bayan da ya kaɗa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe ta ɗaya da ke Ungwan Sarki a yankin ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa.

El-Rufai ya danganta rashin fitowar jama’a zuwa wurin zaɓe da rashin isowar kayan zaɓe a kan kari.

Daga nan, ya yi kira ga talakawansa da su fito ƙwansu da ƙwarƙwatansu don su zaɓi wanda suke so.

Sai dai ya ce, ya lura tsarin zaɓen wannan karon ya fi sauri idan aka kwatanta da zaɓen 2018.

Gwamnan ya yaba da yanayin kayan zaɓen da ya gani wanda a cewarsa babu yadda za a yi a tafka maguɗin zaɓe saboda komai a kimtse yake.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kaɗa ƙuri’ar tasa, an ji gwamnan na cewa su ba za su zama tamkar sauran jam’iyyu ko gwamnatin jihohi ba, “za mu bar jama’ar Jihar Kaduna su zaɓi wanda suke so,” in ji shi.