Goje ya lashe kujerar Sanatan Gombe ta Tsakiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta bayyana Ɗanjuma Goje na Nam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Gombe ta Tsakiya.

Jami’in zaɓe na INEC Farfesa Mustapha Muhammad wanda ya bayyana sakamakon zaɓen a ranar Lahadi a Kumo, ya ce Goje ya samu ƙuri’u 102,916.

Ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Aliyu Abubakar na Jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’u 37,870, da Mista Bibikir Muhammad na Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), wanda ya samu ƙuri’u 1,155.

Goje shi ne ɗan majalisar dattawa mai wakiltar mazaɓar majalisar dattijai kuma ya yi gwamnan Jihar Gombe sau biyu.