Gudunmawar iyaye wajen nasarar ’ya’yansu a makaranta

Spread the love

Tare da BILKISU YUSUF ALI

Iyaye su na da rawar gani sosai wajen tabbatar da nasarar ’ya’yansu a makaranta. Rashin kulawa ko rashin goyon baya daga iyaye kan iya shafar karatun ɗalibai ta hanyoyi da dama, yayin da kulawa da haɗin kai tsakanin iyaye da makaranta ke ƙara wa ɗalibai ƙarfi da ƙwarin gwiwa wajen cimma burinsu. Wannan nazarin za ta bayyana yadda iyaye za su iya taimakawa wajen inganta karatun ’ya’yansu da yadda hakan ke kawo canji mai kyau a rayuwarsu. 

Muhimman abubuwan da iyaye za su yi don taimakawa nasarar ‘ya’ya:

1. Kulawa da yanayin karatu a gida

Iyaye su tabbatar cewa suna samar wa ‘ya’yansu wuri mai kyau da kwanciyar hankali domin karatu. Hakan yana taimakawa wajen mayar da hankali da samun sakamako mai kyau. Ba a iya samun wuri mai kyau ba ne ilimin yara kan inganta ba, hatta unguwa da yaran da ke gewaye da makaranta da irin ɗaliban da ke cikin makaranta suna taka muhimmiyar rawa wurin samar da ilimin yara da tarbiyyarsu. 

2. Taimakawa da kula da aikin gida (homework)

Iyaye musamman mata yana da kyau su kasance masu lura da aikin da ake ba wa yaransu a makaranta. Ba iya aikin da malamai suka bayar ba ne ya kamata iyaye su kalla ko su taya ‘ya’yansu yi ba, a’a a wannan lokaci akwai abubuwa da dama da za su tattauna da ‘ya’yansu kamar jan yaran a jiki don jin labaran ‘yan ajin ‘ya’yansu da jin ya malamansu suke koyarwa kai hatta shigar malaman da wasu mu’amaloli na malaman da ɗaliban duk a wannan zaman ya kamata iyaye su sani. Yin hakan wata dam ace ta shaƙuwa da yara sannan in iyaye suka tarbiyyantar da iyalansu a haka to ko zuwa gaba zai yi wahala ‘ya’yan nan su ɓoyewa iyayensu wasu abubuwa. 

3. Haɗa kai da malamai

Duk lokacin da iyaye suka danƙa ɗansu a hannun malami to wannan amana da sadaukarwa da yarda babu tamkar ya ita don ɗa ba abin wasa ba ne. Don haka yin hulda kai tsaye da malamai na makaranta don samun bayanai game da halin da ɗalibi ke ciki, da yadda za a magance matsalolin da suka taso yana da matuƙar amfani. Ya kamata iyaye su san su wa ye ke kula da tarbiyyar ‘ya’yansu. Gane wannan kuwa kai tsaye sai da bibiya da kai ziyara da halarta tarurruka da makaranta take shiryawa don ganawa da iyayen yara. 

4. Karfafa ‘ya’ya gwiwa

Iyaye su kasance masu ƙarfafa wa ‘ya’yansu gwiwa ta hanyar yabawa a duk lokacin da suka samu nasara ko suka yi ƙoƙari, hakan yana ƙara musu kwarin guiwa. Iyaye kada su zama masu hantara da kushe da ɗari-ɗari ga ‘ya’yansu. Duk lokacin da yaro ya yi kwazo ko ya nuna wata amana ko gaskiya ko jarumta yana da kyau iyaye su yaba masa su yi masa kyauta komai ƙanƙantarta don su ji ɗaɗi. 

5. Horon rayuwa da ladabi

Baya ga karatu, iyaye su koya wa ‘ya’yansu dabi’u masu kyau kamar tsari, kiyaye lokaci, da ladabi  da biyayya da gaskiya da jarumta da dogaro da kai da tawakkali da yin addu’a da sauran ayyuka na gari. Tsarin koyawa yara wannan yana da matakai daban-daban. Wani kai tsaye wata koyarwar ta cikin hikima wata kuma ta hanyar labarai ko tatsuniya wadda za ta nuna sakamakon alheri da sakamakon wanda ya zama marar kirki ko tarbiyya. Wannan  zai taimaka musu wajen yin kyakkyawan aiki a makaranta da kuma rayuwa gaba ɗaya.

6. Cusawa yara aƙidar abin da za su zama a gaba

Iyaye su za su gina tunanin ‘ya’yansu da nuna kishi da ɗorasu a hanyar samun kwarewa a fanni na musamman. Duk da akan samu yara da suke da ra’ayi na musamman to amma waɗannan ba su da yawa. Iyaye in suna son ɗansu ya zama likita to tun yana yaro sai su ke saya masa abubuwan da ya shafi aikin likita ko asibiti. Haka in lauya ne ko ɗan sanda ko soja  ko malamin makaranta da sauran ɓangarori na musamman. Haka in yaro ne ya nuna ga abin da yake son zama kamar injiniya ko kasuwanci iyaye yana da kyau su ƙarfafe shi tun yana ƙarami da taya shi ƙaunar abin da ɗansu yake so don cikar burinsa.  

Tasirin Gudunmawar Iyaye:

ɗalibai  da suke da iyaye masu  kulawa suna samun sakamako mafi kyau a makaranta.

Rage rashin halartar makaranta da jinkiri wajen zuwa yana haifar da gazawar ɗalibi da zama kullum a baya.

Samar da yanayi mai kyau da kwanciyar hankali ga ɗalibi wannan yana ƙara masa ƙwarewa da natsuwa wajen karatu.

Iyaye na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar ‘ya’yansu a makaranta. Ta hanyar nuna kulawa da ƙarfafawa da haɗin kai da malamai, iyaye na iya taimakawa wajen gina ƙarni mai ilimi da nagarta. Haka nan, wannan haɗin kai yana haifar da al’umma mai ci gaba da samar da kwararru a fanni da dama.

By ukarofi