
Ƙungiyar ƴan kasuwa ta Bichi Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited ta kai ziyarar bangirma ga Shugaban Hukumar Zuba Hannun Jari da Kula da Kadarorin Gwamnatin Jihar Kano, Hon. Auwalu Muntari Mai Royal tare da wasu jigogi a cikin al’u,ma.
Shugaban kungiyar, Alhaji Abubakar Mazahim Saleh ya ce ƙungiyar ta ji daɗin irin yadda Shugaban Hukumar Kadarorin Gwamnatin Jihar Kano, Hon. Auwalu Muntari ya tarbe su cikin kulawa.
Ya bayyana cewa sun yi farin ciki da shawarwarin da ya ba su tare da alkawarin da ya yi musu na yin aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ƙungiyar, domin tabbatar da ci-gaban kasuwar da garin Bichi baki ɗaya.
Shugaban, ya yi kira ga ƴan kasuwar da su rubuto buƙatunsu domin dubawa da ba su shawarwari daga ƙwararru tare da nemo hanyoyin magancesu domin bunƙasa kasuwar daga fannin Gwamatin Jihar Kano.
“Sannan mu haɗa da iliminmu na kasuwancinmu, mu ga cewa za mu fito mu yi maganin wadannan matsalolin, sannan mu ga me za mu shigo da shi da taimakon Allah da taimakonku da hadin kanmu, mu ga an gyara wadannan abubuwan a samu masalahar da kasuwancin Bichi zsi habaka, amma lillahi wa rasulihi idan ba mu gayara kasa ba sama ba za ta gyaru ba.”
A sanarwar da jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, ta ce ƙungiyar ta yaba wa Mai ba gwamna shawara akan tsaftar muhalli, Hon. Abdullahi Shehu Bichi da suka ziyarce shi a ofishinsa dake sakatariyar Audu Bako, bisa ɗaukarsa a matsayin uba, jagora sakamakon gudunmawarsa gare ta.
Ya yi alƙawarin aiki tare da su ta hanyar samar da hanyoyin kawar da shara da tsaftace magudanan ruwa da feshin maganin sauro a cikin kasuwar.
“Wannan lamarin idan duk muka kintsu, gaba dayansu za mu nemi alfarma a samu koda spilt loaderce ta shiga kasuwar a yi shara a kwashe duka kazantar nan.”
Haka kuma ƙungiyar, ta kai ziyara offishin mai Bai wa Gwamna Shawara a kan ‘Yan Fansho, Shugaban Kwamitin Dattawa na Jam’iyyar NNPP, kuma kwararre masanin harkar saye da sayarwa da hada-hadar kasa, Hon. Abdullahi Shu’aibu (kosi), inda ya ba su shawarwari a kan hanyoyin da za a bi wajen daga darajar kasuwar ta fuskar kimar shaguna da kuma tsarin kyautata haya a cikinta.
“Kauyikan da suke a kusa watakila idan za su taru su dawo cikin gari, wannan zsi dada taimaka wa garin ya fadada arziki ya yawaita, to wannan shi ne sake bubkasa kasuwanci.”
A wani ci-gaban kuma, ƙungiyar ta ziyarci Shugaban Gudanarwa na Bankin Emaar MFB na Jihar Kano a ofishinsa dake Kabuga, Alhaji Haruna shehu da H.O.D Malam Rabi’u Yahaya Yakasai tare da sauran ma’aikatan bankin, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi kasuwanci da habaka tattalin arzikinsu.
A karshe ‘yan kasuwar sun ziyarci tsohon Shugaban Ma’aikatan Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Mahmud Faruk a gidansu dake Kabara cikin garin Kano, Alhaji Mahmud wanda a yanzu yake aiki a ofishin Hukumar Kula da Kananan Hukumomi ta Jihar Kano, ya yi farin cikin wannan ziyara tare da fatan alheri ga wannan ƙungiya.




