Kano: Bichi ta karɓi baƙoncin kwamitin duba ayyukan ƙananan hukumomi na jihar

Spread the love

Kwamitin Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi da Masarautu na Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ya waiwayi Karamar Hukumar Bichi domin duba ayyukan ci-gaba da ake gudanarwa a yankin.

Ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin, Ɗan Majalisar Bebeji, Hon. Aliyu Muhammad Tiga da sauran tawaga, kwamitin ya zagaya wasu sassa da shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ya gina a yankin.

Wuraren da kwamitin ya kai ziyarar gani da ido sun haɗa da titin burji na Tudun Tuluna zuwa rabawa da makarantar fimare a Hayin Waya tare da kuma gidan masarautar Bichi inda ya yi gyare-gyare a fadar sarki da suka kunshi fenti saka fankoki da na’urar sanyaya daki da kuma sauransu.

Wakilin shugaban karamar hukumar, Sakataren Mulki, Hon. Anas Muhammad Abdullahi, ya ji dadin irin yadda kwamitin ya yaba da ingancin ayyukan da karamar hukumar ta yi kwanannan, sama da talatin a kankanin lokaci.

“Mun ji dadin wannan ziyarar wadda za ta karfafa mana gwiwa wajen yin ayyuka nagartattu da kuma bibiyar ayyukan da ‘yan kwangila suke yi a wannan karamar hukuma tamu, kuma in sha Allahu za mu yi mentenin temfo karkashin jagorancin mai hirma Hon. Hamza Mai Fata domin tabbatar da ayyuka nagartattu wadanda al’uma za su dade suna mora, duk abin da kake bukata ba wai kai me kake so ba? A’a me za a yi wa al’uma wanda za su ji dadi.”

A hannu guda bisa hoɓɓasa, Karamar Hukumar Bichin yanzu haka tana tsaka da farfado da Kwamitin Kar-ta-kwana (EPR Committee) a bangaren lafiya sakamakon matsalar cutuka masu yaduwa dake saurin bulla a yankin domin kiyaye lafiyar al’umar yankin da dakile matsalar baki daya.

Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata kuma shugaban kwamitin, ya haɗa da; Shugaban sashen lafiya, kansilan lafiya, iyayen ƙasa, jami’in lafiya a matakin farko, Jami’in Binciken Lafiya na yankin, Malaman Fadakarwa kan harkokin lafiya.

Sai kuma Baturen ‘Yan Sanda, Jami’in DSS, Jami’in Gudanar da Aikin Rgakafi na Yankin, Jami’in Kula da Mahalli na Yankin, likitan Asibitin Dabbobi na Sashen Gona da wakilan Kungiyar Lafiya ta Duniya, UNICEF da sauransu, kamar Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, wato jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar ta ruwaito.

By Babaji