Gwajin ƙarshen shekara kan ƙoƙarin Bichi da ƙudirin Tinubu na samar da abinci

Spread the love

Daga SHEHU MUSTAPHA CHAJI

Engr. Dr. Rabiu Suleiman Bichi shugaban hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are, Kano da manyan daraktocin hukumar da suka haɗa da Hon. (Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso babban daraktan kuɗi da Alhaji Tijjani Isa babban daraktan tsare tsare da Hajiya Zainab Gamawa babban daraktan noma da Engr. Datti Abdulkadir babban daraktan Injiya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa su kan muƙaman su ranar 18 ga Disamba 2024 suka kama aiki ranar 18th Afrilu – 2025.

Hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are kamar sauran hukumomin raya koguna, ma’aikatu ne na Gwamnatin Tarayya da suke da alhakin kulawa da sarrafa ruwa ƙasa dana ƙarƙashin ƙasa da noman rani da ayyukan da za su bunƙasa cigaba noman zamani da tattlin arziki.

Yayin da Engr. Dr. Rabiu Suleiman Bichi ya kama aiki a hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are domin fahimtar halin da hukumar ke ciki ya fara da ziyartar dama damai da ke ƙarƙashin hukumar a Jihohin Kano da Jigawa da Bauchi.Yayin ziyayar Bichi ya ziyarci gwamnoni da sarakuna da masu ruwa da tsaki a jihohin. Kuma ya tattauna dasu kan batuwuwan da suka shafi samar da abinci da daƙile barazanar da dakatar da zaizayar ƙasa da ambaliya da sabbin dabarun noman zamani da samar da sabbin wuraren noma da sauran su.

Yayin ziyara ne Bichi ya sami damar sani injinan turo ruwa da wuraren tattara ruwa da basa aiki na tsawon lokaci ya kuma bada umarnin a gyara su.

A watanni tara bayan kama aiki Bichi yayi ƙoƙarin kawo canje canjen domin kawo cigaba a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi ta hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are. Salon shugabancin sa ya samar da gagarumin cigaba a mu’amalar ma’aikata da manoma da al’ummar da ke yankin hukumar.

Cikin ayyukan cigaba da ayyukan da za a ƙaddamar a hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are ƙarƙashin jagorancin Rabiu Suleiman Bichi sun haɗa da:

Samar da sabbin dabarun noman zamani a dam ɗin Tiga wanda ya haɗa da kiwon kifi da samar da lantarki da noman rani haɗe da fasahar zamani. Abinda ake a dam ɗin Tiga ana shigen irin su a sauran dama damai da suke ƙarƙashin kulawar hukumar sa.

Ana kuma cigaba da ayyukan titi da zai kai dam din Tudun wada Galala a Ningi Jihar Bauchi domin samun sauƙi wajen fitar da albarkatun noma a yankin da kewaye.

Cigaba da ayyukan gyara da bunƙasa wajen noma a Hadejia Barrage dan bunƙasa noma rani da yawan albarkatun noma.

Duba da kula da ayyukan hakan bore hole bore hole guda 40 dan samar da ruwan sha a babban birnin Dutse Jihar Jigawa da kewaye.

Duba da kulawa da yanda ake haɗa na’urorin noman zamani dan roman rani a Chiromawa/ Kadawa da ke Jihar Kano a gona mai girman hecta casa’in.

Ayyukan samar da magudanan ruwa da kawo ƙarshen zaizayen ƙasa a Jihar Jigawa.

Duba da ayyukan cigaba da aikin dam din Malikawa Garu da faɗaɗa wuraren noma na hecta 6000 a Jihar Kano.

Tsayar da gyaran wuraren da zaizayen ƙasa ya lalata a garin Kau Kau da ke Jihar Kano.

Duba da cigaba da aikin dam din Dunbulum a ƙaramar hukumar Tsanyawa da ke Jihar Kano.

Gyara magudanan ruwa da ke Miga Mashau dan kaucewa ambaliya a wannan yankin da ke Jihar Jigawa.

Cigaba da cire ciyawar kachala dake toshe, tare da jawo ambaliya a magudanan ruwa da hanyoyin ruwa a Jihohin Kano da Jigawa da Bauchi.

Cigaba da ayyukan hakan bore hole bore hole a garuruwa da ƙauyukan da ke jihohin Kano da Jigawa da Bauchi.

Samar da kuma koya wa manoma sabbin dabarun noman zamani da ke buƙatar ruwa kaɗan da sauran su.

Haɗin gwiwa da hukumomin dan bunƙasa noma. Misali haɗin gwiwa tsakanin hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are da hukumar raya yankin Arewa maso Yamma (North West Development Commission) dan bunƙasa noma a yankin Arewa maso yamma.

Da’awar kowane gida ya zama wajen noma (Every Home is a Garden).

Shiri domin koyawa matasa noman zamani na Green House a Jihohin Kano da Jigawa da Bauchi.

Shiri na samar da malaman gona matasa har 500 dan koyawa manoma sabbin dabarun noman zamani.

Ƙudirin samar da sabbin dama damai uku a yankin ƙaramar hukumar Bichi a Jihar Kano.

Hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are ta sami lambar yabo daga hukumar haraji ta ƙasa wato Federal Inland Revenue Service (FIRS) a matsayin hukumar Gwamnatin Tarayya da tafi biyan haraji a Jihar Kano.

Daidaita rigingimun ƙungiyoyin manoma masu amfani da ruwa dan noman rani a jihohin dake ƙarƙashin hukumar.

Ƙoƙarin hukumar wajen samar da tsaro inda ta kammala tare da miƙa makarantar horar da jami’an Civil Defense a Gwarzo Jihar Kano.

Taimakawa wajen samar da bore hole ga barikin jami’an tsaro misali barikin yan sandar kwantar da tarzoma da ke Jihar Kano.

Gwamnonin jihohin Jigawa da Bauchi sun yi alƙawarin aiki da hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are dan bunƙasa noma a jihohin su saboda sun gamsu da shugabanci da gogewar Rabiu Suleiman Bichi musamman a fannonin tattalin ruwa dan bunƙasa noma rani a jihohin su.

Akwai ayyuka da dama na cigaba da aka samu ƙarƙashin jagorancin Rabiu Suleiman Bichi a watanni tara da lokaci ba zai bamu damar lissafo su ba.

Ta ɓangaren siyasa, Rabiu Suleiman Bichi shine babban daraktan kamfen din Gawuna/Garo da Tinubu/Shettima a zaɓen shekarar 2023. Ko bayan kama aiki a hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are ya kasance ya ɗorawa kansa bayyanai kan ayyukan cigaban ƙasa da Shugaba Tinubu ke yi musamman a Jihar Kano da Arewacin Najeriya. Duk lokacin da zai yi jawabi ko tattaunawa da yan jarida sai ya zayyano manufofi da ayyukan cigaban ƙasa da Shugaba Tinubu ke yi. Yayin da yake kan hanyar tafiya duk inda ya tarar da ana aiki yakan tsaya ya jinjina wa ma’aikata da basu ƙwarin gwiwa ya kuma faɗawa al’umma cigaba da ake samu a aikin.

Bichi ya kuma karbi dubban yan siyasa da suka canza sheka zuwa Jam’iyyar APC musamman yan Jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya.

Bichi mutum ne mai hazaƙa dake aiki ba dare ba rana dan cigaban hukumar raya kogunan Hadejia da Jama’are da Najeriya.

A taƙaice Bichi ya ciri tuta ya kuma yi ƙoƙari matuƙa wajen samar da sabbin dabarun noman zamani da samar da yanayin da abinci zai samu ya kuma wadata a Jihohin Kano da Jigawa da Bauchi kamar yanda Shugaba Tinubu ya umarce su yayin ɗora masu wannan aikin.

By ukarofi