Gwamnatin Katsina za ta kafa masana’antar taki a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da kamfanin Al-Hikma Fertiliser and Chemicals Ltd. na jihar Kano domin kafa masana’antar sarrafa taki da kayan noma da kudinta da ya kai Naira biliyan biyu.

Za a gina masana’antar ne a ƙananan hukumomin Ɓatagarawa da Rimi.

An sanya hannu kan yarjejeniyar tsakanin darakta janar na hukumar bunƙasa zuba jari ta Jihar Katsina (KIPA), Alhaji Ibrahim Tukur-Jikamshi, da darakta manajan kamfanin, Bashir Ahmad.

Da yake jawabi bayan rattaba hannun, Alhaji Tukur-Jikamshi ya bayyana cewa gwamnati ta ware hekta 150 na fili a Tashar-Bala da Rimin-Kaura domin aiwatar da aikin. Ya ƙara da cewa an kafa kwamiti kan jaddawalin tsarin Framework for Responsible Inclusive Land-Intensive Agricultural Investment (FRILLIA), tare da sanya hannu kan umarnin zartarwa domin ƙarfafa aiwatar da tsarin.

Ya kuma bayyana cewa an kammala biyan diyya ga masu filaye, tare da samar da muhimman ababen more rayuwa a yankin Eastern Bypass.

Jikamshi tuni an tuntuɓi ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya, kuma sun amince da amfanin aikin ga al’umma.

A nasa jawabin, Bashir wakilin Kamfanin ya ce ana sa ran fara aikin masana’antar a shekarar 2026.

By ukarofi