
Daga BELLO A. BABAJI
Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin gida na Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya jaddada aniyar gwamnatin jihar ta bunƙasa harkar ƙirƙira ta digital da inganta matasa ta fasahar Artificial intelligence, wato AI.
A lokacin da ya kai ziyara a ofishin Afrilab na AI a Zaria, Kwamishinan ya sanya ido kan ayyuka da kayayyakin horo na kamfanin, ya ce abubuwa ne da za su taimaka wa matasa masu tasowa wajen ƙwarewa a ɓangarori daban-daban na AI.
Ya ce ziyarar ta biyo bayan umarnin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar, domin tattauna yiwuwar mayar da ayyukan Afrilab AI Hub zuwa Kano.
A wata takarda da Daraktan Ayyuka na Musamman na Ma’aikatar ya fitar, Kwamishina Waiya ya ce gwamnatin jihar tana ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau ga sabuwar fasahar tare da haɗe ta da ci-gaban fasaha da na tattalin arziƙi.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin za ta bada cikakken goyon baya da tallafin da ake buƙata wajen kafa cibiyoyinta a jihar.

Ya ƙara da cewa samuwar AI a Kano za ta taimaka wajen faɗaɗa hanyoyin ƙwarewa da samar da damammakin ayyuka da kuma mayar da jihar jagora a harkar AI da fasahar dijital.
Kazalika, ya nanata ƙudirin Gwamna Abba na samar da shirye-shirye da za su inganta rayukan matasa musamman ta amfani da fasahar zamani.
A nasa jawabin, shugaban Kamfanin, Abdullahi Shu’aibu Damat ya nuna jin ga ziyarar kwamishinan, ya na mai tabbatar masa da cewa a shirye suke su haɗa kai da gwamnatin Kano don cimma kyawawan manufofinta.