Daga UMAR GARBA a Katsina
Jam’iyyun siyasa biyar ne kawai daga cikin 84 da ake da su a ƙasar nan ake sa ran za su shiga zaɓen ƙananan hukumomi 34 Jihar Katsina wanda za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Katsina (KASIEC) Alhaji Lawal Alhassan Faskari ya shaida wa manema labarai cewa jam’iyyu biyar da suka haɗa da Accord, ADC, Booth, ADP, da kuma APC ne za su shiga zaɓen.
Sai dai manyan jam’iyyun adawa irinsu PDP da NNPP sun bayyana cewar baza su shiga zaɓen ba a bisa dalilai daban daban da suka bayar ciki harda matsalar tsaro, zargin rashin gudanar da sahihin zaɓe da kuma tsadar fom ɗin tsayawa takara.
A cewar jam’iyyar PDP, ta yanke shawarar ƙaurace wa zaɓen saboda tana ganin ba za a yi wa ‘yan takarar jam’iyyar adalci ba.
Asarar kuɗi ne kawai PDP zata yi muddun ta shiga zaɓen ƙananan hukumomin.
Alhaji Bishir Biro Kankia ɗaya daga cikin manyan mambobin jam’iyyar ya yi zargin cewa zaɓen rubutashi kawai za a yi.
“Kwamishinan zaɓe na gwamna, sakataren zaɓe na gwamna, hukumar zaɓe ta gwamna faɗi mani wanda zai iya kada gwamna”? Kamar yadda Kankia ya tambaya.
Ita kuwa jam’iyyar NNPP cewa ta yi kuɗin fom na takarar ya yi mata tsada.
Sakataren jam’iyyar ta NNPP a jihar Katsina Alhaji Tijjani Zakari Kafinsoli ya bayyana wa manema labarai cewa adadin kuɗin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (KTSIEC) ta ƙayyade domin sayen fom ɗin tsayawa takara ya yi yawa ta yadda jam’iyyar ba za ta iya biya ba.
Kafinsoli ya ce, hukumar zaɓe ta jiha ta sanya Naira miliyan 3 a matsayin kuɗin fom ga ‘yan takarar shugabannin ƙananan hukumoni da kuma miliyan 1 ga ‘yan takarar kansila.
“Muna da ƙananan hukumomi 34 da gundumomi 361 a jihar, ma’ana jimillar kuɗin fom ɗin zai kai kimanin naira miliyan 463.
“A matsayinmu na jam’iyyar talakawa, ba za mu iya biyan irin wannan adadin kuɗi ba. Mun rubuta wa KTSIEC a cikin watan Afrilu, 2024 don yin ƙorafi game da yawan kuɗin amma ba mu sami amsa ba”. In ji shi.
Kazalika ita ma jam’iyyar SDP, ta ce ta janye ne daga zaɓen saboda tsadar kuɗin tsayawa takara lamarin da ya kai ga jam’iyyar ta SDP ta maka hukumar zaɓen jihar ƙara a kotu kan wannan batu.
Da yake bayar da amsa game da ƙorafin jam’iyyun adawar kan zargin rashin kwatanta adalci da kuma tsadar kuɗin tsayawa takara shugaban hukumar Alhaji Lawal Faskari ya ce, hukumar tana da ikon ƙayyade kuɗin fom ɗin tsayawa takara saboda haka jam’iyyun da suka janye ba su da wani ƙwaƙƙwaran dalilin yin haka.
A cewar Faskari, hukumar ta kammala shirye-shirye don tabbatar da an gudanar da zaben kamar yadda aka shirya a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025 cikin lumana.
Ya kuma ce hukumar ta saka ranakun 14 da 15 ga watan Fabrairun 2025 don fara rabon kayayyakin zaɓe zuwa mazaɓu.
Faskari yayin da yake ba da tabbacin shirin hukumar na gudanar da sahihin zaɓe a faɗin ƙananan hukumomi 34 na jihar, ya tunatar da ɗaukacin jam’iyyun siyasar dake jihar buƙatar akan su dakatar da yaƙin neman zaɓe sa’o’i 24 gabanin ranar zaɓe kamar yadda dokar hukumar ta tanada.
