Gwamna Ganduje ya ayyana Litinin a matsayin ranar hutun sabuwar shekarar Musulunci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar 1 ga watan Augusta shekara ta 2022 a matsayin ranar hutun domin murnar sabuwar shekarar Musulunci ta 1445 bayan hijrah.

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bada wannan umarnin cikin sanarwar da Kwamishinan Ma’aikatar Yaɗa Labaran Jihar Kano Malam Muhammad Garba ya rattaɓawa hannu, don haka,  sai ya taya al’ummar Musulmin Jihar Kano murna bisa muhimmancin wannan rana tare da buƙatar yi wa kai hisabi.

Ya kuma buƙace su da su yi amfani da wannan hutu wajen neman gafarar Allah, tare da roƙon Allah ya kare Jihar Kano daga matsalar tsaro domin samun ɗorewar zaman lafiya da cigaban Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.

Hakazalika gwamnan ya tabbatarwa da al’ummar Jihar Kano tabbacin ci gaba a cika alƙawuran da ya yi na inganta rayuwarsu ta hanyar samar da shirye-shiryen da za su kyautata rayuwar al’umma.

Sanarwa ta kuma jadadda buƙatar da ake da ita na jama’a kowa ya tabbatar da ganin ya karɓi katin zaɓensa domin sauke nauyin dake kansa lokacin babban zaɓe mai zuwa.

Ana sa ran ganin watan na Almuharramn ranar Asabar 30 ga watan Yulin Shekara ta 2022.