Gwamna Ganduje ya haramta ɗaga tutocin siyasa a masallatan Idi

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta haramta liƙa hotuna da ɗaga tutocin siyasa a lokacin bukukuwan ƙaramar Sallah.

Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya bayyana hakan ta cikin saƙonsa na barka da Sallah ga al’ummar Kano.

Ta cikin saƙon barka da Sallar da Gwamnan ya fitar ta hannun Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Malam Muhammad Garba, ya ce daga yanzu an hana saka tutoci, ko allunan ‘yan siyasa yayin sallar idi da sauran bukukuwan sallah domin kauce wa rikici.

Ya ce, Sallar idi ibada ce muhimmiya bayan azumin Ramadana da ake bin bayanta da bukukuwan bajakolin tarihi da al’adu, wanda ake zuwa kallo har daga ƙasashen waje.

Gwamnan Ganduje ya ce bai kamata a mayar da wuraren Ibadah wajen gangamin siyasa da yaƙin neman zabe ba.

Kazalika ya jaddada cewa, ɗaga allunan siyasa a yayin taron da ya haɗa jama’a masu mabanbantan ra’ayi kamar Hawan Daushe, ka iya haifar da tarzoma.

Sanarwar ta kuma umarci yan siyasa da su tabbatar sun yi biyayya ga sabuwar dokar zaɓen.

Gwamna Ganduje ya taya al’ummar musulmi murnar bikin Sallah, tare da fatan za su yi riƙo da abin da suka koya a watan azumi.

Sannan ya yi kira ga jami’an tsaro da su nuna halin ba sani ba sabo, ga duk wanda ya yi ƙoƙarin tayar da zaune tsaye yayin bukukuwan sallar.

By Editor