Ɗauke Hukumar SON daga tashoshin jirgen ruwa ne sanadin shigo da kaya marasa inganci Nijeriya – Darakta

Daga AMINA YUSUF ALI

Daraktan janar na hukumar tabbatar da ingancin kayayyaki (SON), Farouq Salim, ya bayyana cewa, tattalin arzikin Nijeriya yana qara rugujewa sakamakon kayayyaki marasa inganci da ake shigo da su cikin ƙasar, inda hakan ya faru ne sakamakon ɗauke hukumar daga tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya. 

Daraktan ya yi wannan furuci ne a taron masu ruwa da tsaki da aka yi a Legas mai taken, ‘kaya masu inganci suna ceto rayuka, kuma su bunƙasa tattalin arziki’.

Salim ya ƙara da cewa, in dai kuwa za a cigaba da shigo da waɗancan kaya marasa inganci, to kuwa ƙasar ba za ta kai labari ba ta fannin tattalin arziki. 

A cewar sa, ko da hukumar ta SON wani lokacin take ƙwacen kaya marasa inganci da ‘yan kasuwa suke shigo da su, ai waɗannan ‘yan kasuwar su ake taimaka wa. Amma daga ƙarshe ba wai ga kamfanoni ko ‘yan kasuwar illar abin yake tsayawa ba, har ma da al’umma. 

Inda ya bayyana cewa, babbar matsalar a Nijeriya ba wanda yake Kano irin waɗancan ‘yan kasuwar don a gurfanar da su a gaban kuliya. 

Daga ƙarshe ya yi kira ga ‘yan kasuwa na ƙwarai da su cigaba da shigo da kaya masu inganci cikin ƙasar nan domin matuƙar suka cigaba da shigo da gurɓatattun kaya, to za su lalata wa kansu sana’a. 

Shi ma a nasa jawabin shugaban ƙungiyar jami’an hana fasa ƙwauri/ kwastan (ANLCA), Kayode Farint ya bayya n cewa, shi a nasa ra’ayin yana ganin in dai gwamnati na son yin nasara a kan yaƙi da shigo da kaya marasa inganci, to sai an mayar da jami’an hukumar SON bakin tashar Teku.

A cewarsa, al’amuran sun fi tafiya daidai a shekarun baya lokacin da hukumar SON ɗin tana tashar bakin tekun.