Gwamna Lawal ya taya Musulmin Zamfara shiga sabuwar shekarar 1445

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya miƙa saƙon taya murna ga al’ummar Musulmin jihar dangane da shigowar sabuwar Musulunci ta 1445.

Gwamnan ya yi wa Musulmin jihar, na ƙasa da ma duniya baki ɗaya fatan alheri da kuma murnar ganin sabuwar shekarar, tare da kira a gare su da su duƙufa da addu’ar samun zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa a jihar.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya sanya wa hannu.

Ya ce, “Sabuwar shekarar ta Musulunci na nuni da hijirar da Annabi Muhammad (SAW) ya yi daga Makka zuwa Madinah, kuma al’amari ne mai matuƙar muhimmanci ga Musulunci da Musulmi.

Sanarwar ta nuna irin muhimmancin da Hijirar ke da shi a rayuwar Musulmi ciki har da haɗin kai da son juna da sauransu.

Don haka Gwamnan ya ce, “Ina so in yi amfani da wannan dama wajen kira ga al’ummar Jihar Zamfara da mu haɗa kai wajen kawar da dukkan matsalolin da ke yi wa cigaban jiharmu tarnaƙi. Ina taya ku murnar sabuwar shekarar Musulunci ta 1445.”