Gwamnan Zamfara ya yi wa Dahiru Mangal ta’aziyyar rasuwar matarsa a Katsina

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ziyarci Katsina don yin ta’aziyya ga Shugaban Kamfanin Jirgin Max, Alhaji Dahiru Barau Mangal bisa rasuwar matarsa.

Shahararren ɗan kasuwar ya rasa matarsa Aisha ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata a babban birnin tarayya, Abuja.

Gwamna Lawal a wata takardar manema labarai da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa wacce iyalanta za su yi kewar rashinta matuƙa.

Haka nan ya yi addu’ar Allah Ya yi wa marigayiyar sakamako da masauki a Aljannah.

“Mun zo ne domin yin jaje da ta’aziyya na wannan gagarumin rashi da aka yi. Muna jajanta wa dukkanin iyalai da ‘yan uwa.

“Wannan lokaci ne mai tsanani ga ilahirin iyalan marigayiyar da ma ɗaukacin al’ummar Katsina. Allah Ya ƙarfafe ku da juriyar wannan rashi,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *