Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya gwangwaje ƙungiyar ‘yan jarida wakilai (Correspondent’s Chapels) da Mota ƙirar Bus domin sauƙaƙa kaiwa da komawa wajen nemo tare da yaɗa labarai.
Da yake miƙa maguɗin motar ga shugaban ƙungiyar, Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa ya zama wajibi ga duk wata gwamnati da ta san abinda take yi ta yi aiki kafaɗa kafaɗa da ‘yan jarida wajen yaɗa manufofin ta da aikace aikacen da take aiwatarwa ga alummar.
Gwamnan sai ya yi kira ga manema labarai da su rinƙa taka tsantsan wajen yadda suke yaɗa labarai ga al’umma musamman ganin yadda jihar ke fama da matsalar tsaro.
“Ya zama wajibi ku rinƙa nuna adalci, gaskiya da sanin ya kamata wajen bada rahoto kan abinda ya shafi Jihar Katsina”gwamnan ya ce.
“Babu shakka Jihar Katsina na fama da ƙalubale na tsaro,don ya zama wajibi ku rinƙa sanin ya kamata wajen bada rahoton da ya shafi tsaro.
Tunda farko, shugaban ƙungiyar, Malam Yusuf Ibrahim Jargaba ya miƙa godiyar sa ga Gwamna Raɗɗa bisa kyautar mota ga ƙungiyar da ya ce ya zo a kan lokacin.
Ya bayyana cewa motar da ƙungiyar ke amfani da ita ta wuce shekara 10 wanda ta kai yanzu saboda tsufa ba ta tafiya mai nisa.
Jargaba ya ce wannan sabuwar mota babu shakka za ta sauƙaƙa wa ya’yan kungiyar wajen yaɗa labarai.
