-Majalisar dokoki ta shirya tantance su ranar Juma’a
Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya naɗa sabbin kamishinoni takwas a matsayin wani mataki na ƙarfafa gwamnatinsa da inganta yadda ake gudanar da ayyuka bayan ya sallami wasu kwamishinonin nasa kwanan nan.
Shugaban majalisar dokokin jihar Nasarawa Rt. Hon. Danladi Jatau ne ya sanar da hakan a lokacin wani zama na musamman da majalisar tayi a ranar Laraba, inda ya bayyana sunayen waɗanda aka naɗa a yayin da yake karanta wasiƙa daga gwamnan a zaman.
Kamar yadda kakakin majalisar dokokin ya bayyana waɗanda gwamnan ya naɗa a matsayin sabbin kwamishinonin gwamnatin nasa cewa sun haɗa da: Muhammad Habeeb Nagogo daga ƙaramar hukumar Wamba da Ahmed Yakubu Mohammed daga ƙaramar hukumar Lafiya da Hon. Mohammed Baba Shehu daga ƙaramar hukumar Keffi da Hon. Mohammed Iyimoga daga karamar hukumar Obi da Adamu Rabecca Kpadji daga karamar hukumar Wamba da Nawani Aboki daga karamar hukumar Doma da Jibril Abdullahi Ibrahim daga ƙaramar hukumar Nasarawa da Ashefo Daniel Paul daga ƙaramar hukumar Lafiya.
Kakakin majalisar dokokin jihar Hon. Danladi Jatau daganan sai ya kuma umarci babban sakataren majalisar da ya sanar da waɗanda aka zaɓa tare da neman su kawo kwafi 30 na takardun tarihin aikinsu domin tantancewar da za a yi musu a ranar Juma’a 7 ga watan Agustan din nan da ake ciki na 2026.
Wakilin mu a jihar ya kuma ruwaito cewa an kuma bayyana cewa wannan naɗin nasu zai tabbata ne bayan sun kammala tantancewar da amincewar majalisar dokokin ta jihar.
