Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da rabon buhunan taki sama da 100,000 ga manoman jihar domin noman daminar shekarar 2026, inda gwamnati za ta sayar da takin a rabin farashin kasuwa.
Gwamnan ya bayyana cewa yayin da ake sayar da buhun taki kan Naira 50,000 a kasuwa, gwamnatin jihar za ta sayar wa manoma kan Naira 25,000.
An ƙaddamar da shirin ne a filin sukuwa na Kano, ranar Alhamis tare da halartar shugabannin ƙananan hukumomi 44, kwamishinoni, wakilan hukumomin ICPC da DSS, wakilin ma’aikatar ayyukan gona ta tarayya, sarakunan gargajiya da sauran manyan baƙi.
Za a raba manyan motoci tirela 150 da ke ɗauke da buhunan taki sama da 100,000.
Gwamnatin jihar ta ce kowace ƙaramar hukuma za ta karɓi nata kaso ƙarƙashin kulawar kwamitocin da aka kafa, tare da sa ido daga jami’an tsaro da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa.
A jawabinsa wanda ya wakilci Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, Sarkin Dawaki Bello Tuta ya buƙaci gwamnati ta ƙara tabbatar da tsaro domin bai wa manoma damar gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali.
Shugabar ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Kano, Sa’adatu Soja, ta yaba wa gwamnatin jihar kan samar da taki mai rahusa ga manoma.
Ta ce, “Musamman mu da muke maƙwabtaka da Jihar Plateau, damina ta yi nisa a yankunanmu, kuma manoma na matuƙar buƙatar taki a wannan lokaci.”
Shi ma kwamishinan ayyukan gona na Jihar Kano, Dakta Danjuma Mahmood, ya ce shirin ya zo a daidai lokacin da manoma ke buƙatar taki, yana mai fatan za su yi amfani da shi yadda ya kamata.
Ɗaya daga cikin manoman da suka amfana, Sani Abubakar, ya gode wa gwamnatin jihar, yana cewa shirin na rage wa manoma nauyin kashe kuɗi wajen sayen taki.
Ya ce, “A duk lokacin da aka fara wannan shiri muna farin ciki, domin muna samun taki a farashi mai sauƙi fiye da na kasuwa. Wannan na ƙara mana ƙwarin gwiwa wajen noma.”
