Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai wata muhimmiyar ziyara ta aiki ga takwaransa na Jihar Jigawa Umar Namadi a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Dutse.
Ziyarar ta kasance a matsayin wani bangare na kokarin kara dankon zumunci da inganta hadin kai tsakanin jihohin Kano da Jigawa musamman wajen tattauna hanyoyin bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummar jihohin biyu.
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun mayar da hankali kan muhimman batutuwa da suka shafi ci gaba mai dorewa tsaro da samar da ayyukan yi tare da jaddada bukatar kara hadin gwiwa domin cimma muradun jama’a.
Da yake maraba da bakon nasa, Gwamna Namadi ya bayyana matukar farin cikinsa bisa wannan ziyara yana mai cewa irin wannan hulda tsakanin shugabanni na jihohi na da matukar tasiri wajen karfafa hadin kai, zaman lafiya da cigaban yankin Arewa gaba daya.
Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewa irin wannan mataki na hadin gwiwa na nuna kudirin gwamnatocin jihohi wajen hada kai domin tinkarar kalubale tare da samar da cigaba mai anfani ga al’umma.
