Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Fitacciyar jarumar fina-finan Nijeriya ta Nollywood, Doris Ogala, ta janyo cece-kuce bayan ta bayyana wasu abubuwa masu tayar da hankali game da rayuwarta a wani taron ibada a coci.
Jarumar ta bayyana abubuwan da ta ce sun faru da ita tun tana ƙarama, ciki har da kwana a ɗaki guda da gawarwaki biyu da kuma faɗowa daga saman rufi zuwa cikin daji amma ta tsira.
Yayin da take jawabi gaban mabiya cocin, Ogala ta bayyana kanta a matsayin mutum mai tsananin taurin rai a lokacin yarinta. Ta ce faɗowa daga saman rufi zuwa cikin daji, kuma Allah ya kiyaye rayuwarta. Haka kuma, ta taɓa kwana a ɗaki guda da gawar mutane biyu, tana mai cewa da gaske da Allah bai kiyaye ta ba, da wataƙila ba za ta tsira ba zuwa washegari.
Ta bayyana cewa ta yi imanin Allah bai ɗauki ranta ba ne saboda akwai abubuwa da za ta yi a gaba. A cewarta, ba ta san dalilin da ya sa aka kawo ta wurin ba ko me ya sa take magana, amma tana ganin ita kanta hujja ce ta ikon Allah a rayuwarta.
Jarumar, wadda ta halarci taron ibadar tare da mahaifiyarta, ta kuma yi magana mai cike da tausayi game da soyayyar da take yi wa mahaifiyarta. Ta ce a baya tana rayuwa ne domin faranta wa mahaifiyarta rai, amma yanzu tana rayuwa domin Allah. Ta bayyana mahaifiyarta a matsayin jaruma a rayuwarta, saboda yadda ta tsaya mata duk da suka da hukuncin da wasu ke yi mata.
Ogala ta ce, idan Allah bai hukunta mutum ba, babu wanda zai iya hukunta shi. Ta ƙara da cewa ta rasa abubuwa da dama a rayuwa, amma mahaifiyarta ta kasance ginshiƙi gare ta, domin ba ta taɓa juya mata baya ba duk da ƙalubalen da ta fuskanta.
A yayin jawabin, ta kuma yi wasu zarge-zarge da suka shafi wani fasto, Chris Okafor, inda ta yi iƙirarin cewa ya taɓa amfani da wata mata domin shirya shaidun ƙarya a coci. Wannan ya ƙara janyo sabuwar muhawara kan rikicin da ke tsakaninsu. A baya dai, jarumar ta taɓa zargin faston da karya alƙawarin aure bayan wata dangantaka da ta ce ta fara tun 2017, lamarin da ya tada ƙura a kafafen sada zumunta.
A ƙarshe, Doris Ogala ta jaddada cewa tana da yaƙinin Allah har yanzu yana da manufa a rayuwarta, kuma tsirarta daga haɗurra daban-daban alama ce cewa rayuwarta ba ta zo ƙarshe ba.
Jawabin nata ya janyo ra’ayoyi mabanbanta a shafukan sada zumunta, inda wasu suka nuna damuwa da abin da ta faɗa, wasu kuma suka kallace shi a matsayin shaidar bangaskiya da nazari kan rayuwa.
Ko da yake mutane sun bambanta ra’ayi kan maganganunta, jarumar ta tsaya tsayin daka kan cewa duk wahalhalun da ta tsallake sun nuna cewa rayuwarta na da wata muhimmiyar manufa a gaban Allah.
