Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Jiragen ƙasa na Nijeriya (NRC) ta fitar da rahoton wucin-gadi kan hatsarin da ya afku ga jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja a tashar Asham.
Jirgin KA-2 ya tashi daga tashar Rigasa da misalin ƙarfe 7:15 na safe kamar yadda aka tsara. Ya isa tashar Jere minti guda kafin lokaci, wato 8:52 na safe, sannan ya sake tashi daga nan da ƙarfe 8:59 — jinkiri na minti shida sakamakon haa wani injin jirgi domin ƙara ƙarfin tafiya.
Da misalin 9:16 na safe, yayin da jirgin ke kusa da tashar Asham (kilomita 50–51), an ji wata ƙara mai ƙarfi bayan injin jan jirgi da wani injin da ke biye da shi sun bugu da ɗaya daga cikin dakunan fasinja. Rahoton farko ya nuna matsala ta faru ne a na’urar haɗa dakunan jirgi (coupler). Duk da haka, babu wani ɓangare na jirgin da ya fice daga layi, kuma har yanzu ba a tabbatar da dalilin rabuwa ko sakacin hain ba.
Daga baya an cire wasu sassan da suka shafi hatsarin, ciki har da injin jirgi mai lamba 2809, motar samar da wutar lantarki BVA0002 da kuma ɗaya daga cikin karagon fasinja na SP0006.
Bayan gyare-gyare na gaggawa, jirgin ya bar wurin da ƙarfe 9:42 na safe, ya isa Kubwa 10:10, sannan ya isa tashar ƙarshe ta Idu da 10:39 na safe. Jimillar jinkirin da aka samu minti 38 ne.
Mutane 481 ne gaba ɗaya ke cikin jirgin a lokacin lamarin. Cikin su akwai fasinjoji 429 da suka hau jirgin daga cikin 459 da suka yi rajista, ma’aikatan jirgi 10, jami’an tsaro 26, masu sayar da abinci 6, masu tsaftace wuri 8 da kuma ma’aikatan waje biyu ciki har da jinya.
Rahoton ya nuna cewa mutane 26 sun samu raunuka daban-daban, ciki har da fasinjoji, ma’aikatan lafiya, jami’an tsaro da masu tsafta. An ba su kulawar likitoci nan take.
Bayan da aka shawo kan matsalar, sabis ɗin jirgin Abuja–Kaduna ya ci gaba da aiki, inda jirgin AK1 ya tashi daga Idu zuwa Rigasa da ƙarfe 2:48 na rana maimakon 11:00 na safe. Ya isa Rigasa, Kaduna da 5:33 na yamma, tare da Manajan Daraktan Kamfanin Jiragen ƙasa, Kayode Opeifa, da wasu manyan jami’ai a ciki.
Daga bisani jirgin KA-4 ya sake tashi daga Rigasa da 6:12 na yamma, ya isa Kubwa da 8:31 na dare sannan ya isa tashar Idu da ke Abuja da 8:58 na dare, lamarin da ya nuna cewa ayyukan jirgin sun dawo kan hanya bayan hatsarin.
