Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya caccaki gwamnatin tarayya kan yadda take ɗaukar mataki game da sabbin hare-haren da ake kai wa a Borno, musamman bayan fashe-fashen boma-bomai a Maiduguri.
Fashe-fashen sun faru ne a ranar Litinin wanda aka kai kan al’umma a cikin garin Maiduguri a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri (UMTH) da kasuwar Monday Market ofishin aika saƙonni.
Wannan hari ya haifar da fargaba sakamakon ɓullar sabbin hare-hare a yankin Arewa maso gabas.
A cewar rahotannin farko, aƙalla mutane 5 aka kashe a yayin da wasu da dama suka jikkata. Jami’an tsaro sun ce suna zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai harin waɗanda suka daɗe suna addabar yankin.
Daga baya an tabbatar da cewa an kashe mutane 23 da raunta mutane 108.
Sabon harin dai an kai ne a lokaci guda da wasu hare-hare a Ajari da Baga da Damboa wanda sa jami’an tsaro rarraba hankalinsu a wurare daban-daban.
Haka kuma an kai wani harin a garin Ngoshe da ke ƙaramar hukumar Gwoza wanda ake zargin ‘yan Boko Haram da ISWAP ne suka kai inda suka kashe sojoji da sarakuna da wasu shugabannin garin ciki har da wata mata. Haka kuma sun sace mata da ƙananan yara.
A yayin da yake magana kan lamarin a ranar Talata, sanata Ndume ya yi gargaɗin cewa gwamnatin tarayya tana gab da rasa yarda da al’umma suka yi mata idan ta gaza samar da tsaro da kula da walwalarsu.
Ya kuma ce gwamnatin shugaba Tinubu ta karkatar da hankalinta kan al’amuran zaɓen 2027 a maimakon kula da mummunan halin rashin tsaro da ƙasar nan ke fama da ita.
“Kamar ma mun manta da al’umma ne mun rungumi siyasa a yayin da mutanen da za su zaɓe mu suke mutuwa.”
Sanata Ndume ya gargaɗi APC kan cewa idan suka ƙi kulawa da walwala da tsaron al’umma za su iya rasa yarda da mutane suke da ita a kansu.
“Idan babu wani yunƙuri na kyautata jin daɗi da tsaro, mutane na iya ɗaukar gwamnatin a matsayin maƙiyiyarsu,” ya faɗa tare da neman shugaban ƙasa ya ɗauki lamarin da muhimmanci.
Ya yi kira ga jami’an tsaro kan su ƙarfafa hanyoyin tattara bayanan sirri da matakan daƙilewa. Kuma lallai ne a gano waɗanda suka kai harin bam ɗin Maiduguri da hukunta su. Ya ce za a iya gano wanda ya kai bam ɗin da ya fashewa saboda an ɗauki shi a babur mai ƙafa uku wanda hakan zai tallafa wa binciken da ake na gano waɗanda suke da hannu.
Ndume ya ce matakin da gwamnatin tarayya ke ɗauka bai isa ba.
“Bai isa ba,” ya faɗa.
Ya ce, idan aka yi la’akari da girman tashe-tashen hankula a Borno da sauran wurare. Don haka, ya buƙaci shugabanni, musamman mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da ya kai ziyara jihar tattaunawa da al’ummar da lamarin ya rutsa da su idan shi shugaban ƙasa ba zai samu iko ba.
Tun shekarar 2009 ne ‘yan Boko Haram suka fara kai hare-hare a Borno. Duk da cewa jami’an tsaro sun samu gagarumar nasara, amma har yanzu lamarin na ci gaba da addabar al’umma.
Ana zargin harin baya-bayan nan na da alaƙa da Boko Haram a ƙarƙashin jagorancin Ali Ngulde da ke Gwoza.
Ngulde shi ake zargi da hannu kan hare-haren baya-bayan nan da suka haɗa da na Pulka wanda ya jawo mutuwar sojoji 5 da hare-hare ƙunar bakin wake da wasu mata suka kai su huɗu a Mararaban Gwoza da Pulka wanda ya jawo mutuwar mutane 21.
