Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya Kaddamar da cibiyoyin kula da yara masu tamowa, ya yi gargaɗi Kan karkatar da abincin da ake bada wa.
Sabbin cibiyoyin guda biyu a garin Ɓaure, da Daura, da kuma wuraren jinya (OTP) guda 60 a ƙananan hukumomin 12, wani muhimmin mataki na ƙara ƙarfafa yaƙi da matsalar tamowa a faɗin jihar.
Shirin samar da cibiyoyin ya gudana ne ƙarƙashin kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa wanda zai kula da magance lalurar yara masu fama da karancin abinci mai gina jiki (Tamowa).
A jawabin maraba, ahugaban ƙaramar hukumar Baure, Hon. Saminu Sulaiman, ya bayyana farin cikinsa bisa zaɓen Ɓaure a wannan şhiri, yana mai cewa al’ummar yankin za su amfana matuƙa da cibiyar da aka kafa. Ya ƙara da gode ma gwamnatin jihar Katsina na gyara tare da haɓɓaka asibitocin mazaɓun ƙaramar hukumar.
A nata jawabin, shugabar kwamitin gwamnatin Jihar Katsina na kula da matsalar tamowa, Hajiya Rukayya Hamza, ta bayyana irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen rage matsalar a dukkanin sassan jihar. Ta jaddada cewa an faɗaɗa cibiyoyin jinya tare da ƙara wuraren OTP domin kawo magani kusa da al’umma.
Ta kuma yabawa ƙungiyoyin Médecins Sans Frontières (MSF) da UNICEF bisa gudunmuwar da suke bayarwa wajen tallafa wa şirin a jihar Katsina.
Haka zalika, wakilan Médecins Sans Frontières da UNICEF sun yaba da jajircewar gwamnatin Katsina wajen ba da fifiko ga lafiyar yara, tare da alƙawarin ci gaba da haɗin gwiwa domin rage yawaitar matsalar tamowa.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa wannan ƙaddamarwa cika alƙawari ne da ya ɗauka na yaƙi da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a jihar, yana mai cewa gwamnatin sa ba za ta zuba ido yara na fama da wannan matsala ba tare da ɗaukar mataki ba.
Malam Dikko Raɗɗa ya ce sabbin cibiyoyin za su samar da kulawa ta musamman kyauta ga yara masu fama da matsanancin rashin abinci, yayin da wuraren Outpatient Therapeutic Programme (OTP) guda 60 da aka buɗe a ƙananan hukumomi 12 za su taimaka wajen gano cutar da wuri da kuma ba da magani kusa da jama’a.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin sa ba za ta lamunci mutuwar yara daga cututtukan da za a iya magancewa ba, tare da yin gargaɗi mai ƙarfi kan karkatar da kayan tallafin abinci na musamman (RUTF).
Ya sanar da kafa kotunan tafi-da-gidanka domin hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen karkatarwa ko sayar da kayan tallafin, yana mai cewa babu wanda za a yi wa rangwame, ma’aikacin lafiya ne ko wani ɗan kasuwa.
Gwamna Raɗɗa ya kuma yaba da gudunmawar kwamitoci da abokan hulɗa na cikin gida da na ƙasashen ƙetare, musamman Médecins Sans Frontières da UNICEF, bisa rawar da suke takawa wajen tallafa wa gwamnati.
Ya ƙara da cewa nasarar yaƙi da matsalar tamowa na buƙatar haɗin kai tsakanin gwamnati, ma’aikatan lafiya, shugabannin al’umma da kuma jama’a baki ɗaya.
Ya ayyana cibiyoyin da aka ƙaddamar da kuma wuraren OTP a matsayin waɗanda suka fara aiki a hukumance, tare da kira ga jama’a da su yi amfani da su domin ceton rayukan yara.
Bayan ƙaddamar da cibiyar ta garin Ɓaure mai ɗauke da gadaje 18 na jinyar yara Gwamnan ya kuma ƙaddamar da ɗaya cibiyar ta garin Daura.
