Rigimar fili: Wakilin jaridar Pilot a Nasarawa ya koka a kan kai wa iyalansa hari

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Wasu miyagun mutane da ba a san ko su wanene ba ko daga ina suka fito ba su kimanin mutum 30 sun yi barazanar kai hari ga iyalan wakilin jaridar Pilot a jihar Nasarawa wato Mr. Augustine Kuza akan rigimar Fili a ƙauyen Kuduku dake ƙaramar hukumar Keana a Nasarawa.

Da yake bayyana yadda lamarin ya auku ga ‘yan jaridar ‘yan uwansa Cif Augustine Kuza yace maharan suna jayayya ne akan wani filin noma dake yankin Iwagu da Kuduku duk a ƙaramar hukumar ta Keana a jihar.

Wakilin jaridar Pilot ɗin ya ƙara da cewa bayan matar mai suna Judith Kuza da ‘ya’yanta 6 suna aiki a gonar sai miyagun mutanen suka riske su a gonar inda suka kuma yi musu barazanar kisa idan suka sake dawowa.

Yace “Ni da iyalai na mun daɗe muna noma a gonar shekaru aru-aru kuma mahaifina Kuza Adom da ya mutu yana da shekaru 91 a shekarar 2021 shima yayi noma a gonar amma a yau suna neman fitina da mu dalilin gonar.

“A tsakiyar bara sun gayyato wasu Fulani makiyaya su zauna a filin da ake jayayyar tare da amincewar al’ummar Keana.

” Akan haka yasa muka sanar da ‘yan sanda dake nan garin Keana inda su kuma suka ce filin sun yi magana da Fulanin su kuma Fulanin suka yi alƙawarin cewa za su bar gonar amma sai suka ƙi tafiya.

“Daga bisani sai muka gano cewa ashe Fulanin sun ba wa wasu mutanen Keana ɗin kuɗi ne don su kyale su su cigaba da zama a wajen inda a yanzu suke zarginmu cewa ‘yan garin Kuduku din baƙi ne dake zaman cirani a jihar.”

Bincikan wakilinmu ya gano cewa a yanzu haka mazauna ƙauyen Kuduku duk suna zaman fargaba ne a yanzu don za a iya sake kai musu hari a koyaushe.

A nasa ɓangaren da aka tuntuɓe shi don jin ta bakinsa game da lamarin shugaban ƙaramar hukumar Keana Hon. Adamu Aboki yayi alƙawarin shawokan rigimar inda ya ƙara da cewa tuni ya umurci masu sarautar al’umma a wannan yanki su gaggauta gudanar da cikakken bincike kafin ya dawo daga tafiya da yayi zuwa Abuja.

Shima da aka kirashi don nasa jawabin game da lamarin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar SP Rahman Nansel yace har zuwa lokacin hada labarin nan rundunar ba ta samu labarin yinƙurin harin ba.

Amma ya nanata cewa a kai ƙarar a ofishin ‘yan sandan shiyar karamar hukumar Keana inda lamarin ya auku.

By ukarofi