
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina ya bayar da gudunmawar Dala 10,000 don sake gina wani masallacin juma’a da ya rushe a garin Damagaram na Jamhuriyar Nijar.
Masallacin dai na da daɗaɗɗen tarihi wanda aka gina shi shekaru 200 da suka gabata.
Gwamna Raɗɗa ya bada gudunmawar ne ta hannun Mai ba shi shawara kan harkar siyasa, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo, wanda ke riƙe da sarautar Turakin Damagaram.
Yayin da ya ke bayyana godiyarsa ga Raɗɗa bisa gudunmawar, Mai Alfarma Sultan na Damagaram, Alhaji Abubakar Sanda Umaru, ya ce tallafin zai taimaka matuƙa wajen sake gina masallacin.
Ya bayyana dangantkar da ke tsakanin Katsina da Damagaram wadda ta kai tsawon shekaru 500.
A nasa jawabin, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo, ya shaida wa Sultan Umaru Sanda cewa Gwamna Dikko Raɗɗa ya bada gudunmawar ne saboda kishinsa na ci-gaban addini da ɗorewar dangantaka tsakanin al’ummar Katsina na jihar Damagaram.
“Mai Girma Gwamna, Malam Dikko Umar Raɗɗa, yana da kishin ci gaban zamantakewa da addini da addinin musulunci a jihar Damagaram da Jamhuriyar Nijar baki ɗaya.”
Gwajo-gwajo ya ƙara da cewa, masallacin zai taimaka wajen cusa tarbiyyar addinin Musulunci acikin al’umma wanda kuma hakan zai taimaka wajen magance matsaloli da dama a cikin su.
“Mu mutane ɗaya ne da turawa suka raba tsakaninmu, shi ya sa ya kamata mu ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin al’ummarmu kuma mu haɗa kai wajen magance ƙalubalen da muke fuskanta baki ɗaya.”
