Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ta’addanci da satar mutane don neman kuɗin fansa sune suke barazana da ci-gaban tattalin arziƙin Arewacin Najeriya.
Tsohon shugaban hukumar inganta samar da man fetur ta ƙasa (PTDF) Injiniya Muttaƙa Rabe Darma ya faɗi haka a wajen taron gamayyar ƙungiyoyin saƙa na Arewacin Nijeriya da ya gudana a Katsina.
A cewar sa, kamar yadda na’ura mai hangen wurin da ake aikata laifin nuna, mutane fiye da 10,000 ne suke mutuwa a Arewa ta gabas da yammacin Nijeriya a kowace shekara tun daga shekarar 1914.
Injiniya Rabe ya ce, wannan matsala ta haifar da koma-baya ga harkar noma da ilmi a yankunan inda yara da dama ba su zuwa makaranta.
Haka ma wasu matsalolin suna da alaƙa da ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa da kuma halin matsin rayuwa.
Ya bada shawarar matakai da gwamnatocin Arewa ya kamata su ɗauka don shawo kan matsalolin.
Wasu daga ciki sun haɗa da; haɗin-kai tsakanin ƙungiyoyin al’umma da jami’an tsaro na unguwanni da na garuruwa a matakin jiha don tabbatar da tsaro a yankunansu.
Haka kuma gwamnati ta shigo da tsoffin jami’an tsaro da sukai ritaya domin bada tasu gudunmawar ta hanyar bada bayanai na sirri da za su taimaka.
Injiniyan ya kuma yi kira ga hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) da ta sai ido sosai wajen yadda ake shigo da magunguna a ƙasar da ƙayyade irin magungunan da ya kamata a ke shigowa da su.
Kazalika, ya nemi a ƙara ƙirƙiro cibiyoyin koyon sana’o’i da horas da matasa koyo da zai rage zaman banza.
A ɓangaren ilimi kuwa ya bayyana takaicinsa kan yadda ƙididdiga ta nuna yara fiye da miliyan 10.5 a Arewacin Nijeriya ba sa zuwa makaranta wanda ya ce babban barazana ce ga tsaro a yankin.
Sai ya bada shawarar cewa, gwamnatocin jihohin Arewa su bai wa shugabannin makarantu umarnin su riƙa sanya al’ummar yankinsu cikin al’amuran da suka shafi tafiyar da makarantunsu.
Daga ƙarshe, ya ce ya zama dole manyan Arewa su zo su haɗe-kai wajen ceto yankin daga halin da ta shiga.