
Daga BELLO A. BABAJI
Jam’iyyar PDP reshen Kano ta zaɓi Alhaji Ado Kibiya a matsayin sabon shugabanta na jihar.
An gudanar da taron naɗin ne a Filin wasa na Pillars da ke Sabon Gari a jihar, inda aka bai Ado Kibiya muƙamin, wanda tsohon kwamishinan noma ne a zamanin mulkin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso na farko (1999-2003) inda ya samu goyon bayan mafi yawa daga cikin mambobin jam’iyyar.
Kasancewar sa mai biyayya da kuma ƙwarewa a harkar siyasa, jami’yyar tana fatan Ado Kibiya ya kai ta gaci.
Sabon shugaban ya doke abokin karawarsa, Nuhu Nura ne da wani ɗan takarar kujerar da mafi rinjayen nasara.
Tuni dai aka rantsar da shi don kama ragamar aikin jagorancin jami’yyar.
