
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya ce, gwamnati kaɗai ba za ta iya ɗaukar ɗawainiyar ilimantar da yara ba, yana mai jaddada buƙatar haɗin-gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki domin bunƙasa harkar ilimi.
Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da wani katafaren gini da Hukumar Gudanarwar Christian Academy ta samar a Ungwan Bulus da ke Sabon Tasha a Kaduna, inda Kwamishinan Shari’a kuma Antoni Janar na Kaduna, Dakta James Kanyip ya wakilce shi.
Uba Sani ya ce, samun ci-gaba mai ma’ana a fannin ilimi na buƙatar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, al’umma, ƙungiyoyin addini da kuma cibiyoyi masu zaman kansu.
Ya bayyana cewa, “Aikin ilimantar da yaranmu ba zai iya kasancewa nauyin gwamnati kaɗai ba,” yana mai ƙara da cewa haɗin kai tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki zai taimaka wajen samar da ingantaccen ilimi ga yara.
Gwamnan ya kuma yaba wa masu kafa makarantar bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen haɓaka ilimi, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafawa shirye-shiryen da za su inganta ilimi da ci-gaban matasa a Kaduna.
